Posts

Showing posts with the label NAHCON

Shugaban Hukumar NAHCON Ya Bayyana Cigaban Da Ya Samar Cikin Kwanaki 100, Ya Bukaci Maniyyata Su Ba Da Hadin Kai – Daga Nura Ahmad Dakata

Image
Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana muhimman nasarorin da hukumar ta samu a karkashin jagorancinsa a cikin kwanaki 100 na farkon jagorancinsa   A wata tattaunawa ta musamman da wakilinmu a Kano Farfesa Sale Usman, ya jaddada muhimmancin koyi da shugabancin da ya gabata, inda ya ce, “A rayuwa duk wanda ya riga ka mulki, ko ya yi kura-kurai, ko ya yi nasara, sai ka yi addu’a Allah ya karba nasa ayyukan alheri kuma ya gafarta masa kurakuransa. Muna yin iya kokarinmu a yanzu kuma muna addu’ar Allah Ya taimakemu mu ci gaba da tafiya kan hanya madaidaiciya”.   Ya kuma bayyana cewa shugabancinsa yana daukar darasi daga ayyukan magabata, da amfani da nasarorin da suka samu da kuma gujewa kura-kuransu.   Da yake yin tsokaci kan hakan, ya ce, “A cikin kwanaki 100 da muka yi muna shugabanci, mun cimma yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama na rage farashin tikitin jirgin sama idan aka kwatanta da wanda aka biya a bara. ...

Yadda Farfesa Abdullahi Sale Ya Kawo Sauyi A Harkokin Aikin Hajjin Najeriya - Daga Nura Ahmad Dakata

Image
A wani gagarumin yunkurin kawo sauyi, harkar aikin Hajji na fuskantar  sauye-sauye a karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi Sale Usman, shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON). A cikin kankanin lokaci da aka nada Farfesa Usman, ya kafa sabon ma’auni na kirkire-kirkire, inganta aiki, da rikon amana a tafiyar da ayyukan Hajji da Umrah a Najeriya. Sake Tsara Ayyuka: Daya daga cikin manyan gyare-gyaren da Farfesa Usman ya bullo da shi, shi ne kokarin kawo sauyi kan tantance maniyyata aikin Hajji ta amfani da na’ura. Mahajjata nan gaba kadan za su iya yin rajista ba tare da wata matsala ba ta hanyar da aka samar na yanar gizo, tare da rage cikas da tabbatar da gaskiya. Haka nan,  tsarin yana nuna hakikanin matsayin biyan kudin da maniyyaci da neman biza, da shirye-shiryen tafiya, yana ƙarfafa mahajjata da mahimman bayanai kamar a tafin hannunsu.   Matakan Rage Farashi: Bisa la'akari da nauyin kuɗi da ke kan masu zuwa aikin hajji, Farfesa Usman ya ba da fifiko kan...

Zulum Vows to Enhance Pilgrims’ Experience in Nigeria

Image
Borno State Governor, Professor Babagana Umara Zulum, has reaffirmed his administration’s dedication to improving Hajj operations in Nigeria, highlighting the need for world-class services to ensure a fulfilling pilgrimage experience. The governor made the pledge during a courtesy call from the Chairman of the National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON), Professor Abdullahi Usman Saleh, and his delegation at the Government House in Maiduguri. Zulum lauded NAHCON's strides in managing Hajj activities effectively and assured the commission of his administration’s unwavering support in fostering both the welfare and spiritual enrichment of Nigerian pilgrims.

Tsohon Shugaban NAHCON Ake Bincika Ba Farfesa Abdullahi Sale Usman Ba - Ibrahim Abubakar

Image
Mun lura a matsayinmu na ‘yan kasa masu bibiyar harkokin da suka shafi jin dadin alhazan Najeriya kan batun wani gajeren fafen bidiyo mai cike da radani dake yawo a dandalin sada zumunta kan taron jin ra’ayoyin jama’a wanda kwamitin kula da harkokin aikin haji na majalisar wakilai ya shirya a ranakun 13 da 14 ga watan Nuwamban 2024 da muke ciki kan binciken aikin Haji na 2024, inda shi wanda ya yada wannan fefen bidiyo bai fito karara ya bayyanawa mutane shin tsohon shugaban hukumar NAHCON ko sabon ake bincika. A sanarwar da babban jami’in tawagar tallafawa harkokin yada labarai ga hukumar NAHCON na kasa, Ibrahim Abubakar ya sanyawa hannu, yace, muna so mu sanarwa da jama’a musammam masu shirya wannan makirci, cewa shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman ba ya cikin wannan badakala da ta faru lokacin aikin Hajin 2024, a takaice shi an nada shi shugabancin hukumar ne watanni bayan gudanar da aikin aikin Hajin 2024. Ibrahim ya ci gaba da cewa Zuwan Farfesa Abd...

NAHCON: Unauthorized Contracts Will Not Be Honored

Image
Information has reached the National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) that some persons or self acclaimed agents are using the Commission’s name to make commitments to Service Providers for contracts on pilgrims’ accommodations and feeding arrangements in Saudi Arabia for the 2025 Hajj. Some of these individuals have gone to the extent of making contacts with the Saudi Ministry of Hajj and Umrah in the name of the Commission.  In a statement signed by the Assistant Director Public Affairs of the Commission, Fatima Sanda Usara, said, the Chairman of the Outfit, Prof Abdullahi Saleh Usman, wishes to inform the general public, and all stakeholders within the country and beyond, that NAHCON has NOT authorized any individual, group, or agent to enter into contracts or make any arrangements or agreements on its behalf whether in Nigeria or in Saudi Arabia for the year’s Hajj. NAHCON strictly conducts all official transactions through its recognized and authorized personnel...

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale, Zai Fara Aiki A Matsayin Shugaban Riko Kafin Majalisar Dattijai Ta Tabbatar Da Nadinsa

Image
Farfesa Abdullahi Sale Usman wanda aka nada a matsayin shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON, zai fara gudanar da aikinsa a matsayin Shugaban riko har sai majalisar dattawa ta amince da nadin.  Wannan tsari dai zai kasance har sai majalisar dattawa ta dawo daga hutu domin tattaunawa kan nadin nasa. Hakan na kunshe ne a wata takarda da jaridar Hajj Chronicles ta gani, mai kwanan wata 5 ga Satumba 2024, kuma mataimakin shugaban ma’aikata a ofishin mataimakin shugaban kasa, Ibrahim Hassan Hadejia ya sanya wa hannu.  Wasikar ta bayyana cewa Farfesa Usman zai sa ido kan ayyukan Hukumar yayin da yake jiran amincewar majalisar dattawa. Nadin Farfesa Usman ya samu gagarumin goyon baya saboda dimbin gogewa da gudummawar da ya bayar a fannin aikin Hajji a Najeriya, musamman a jahar Kano lokacin da ya rike matsayin shugaban Hukumar Alhazai ta Kano  Ana sa ran tabbatar da shi a zaman majalisar da zarar ta koma hutu

Shugaban Hukumar NAHCON Farfesa Pakistan: Mahimman Bangarorin Mayar Da Hankali, Kalubale, Da Fatan Gudanar Da Aikin Hajjin Nijeriya

Image
    Daga Nura Ahmad Dakata   Nadin Farfesa Abdallahi Saleh Usman Pakistan a matsayin shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON ya haifar da tattaunawa kan alkiblar gudanar da aikin Hajji a Najeriya nan gaba.     Yayin da nan ba da dadewa ba zai karbi ragamar jagoranci, bangarori da dama da suka fi mayar da hankali, da kalubalen da za su iya fuskanta, da kuma fatan cimma burin da aka sa gaba, an gano su daga masu ruwa da tsaki a harkokin aikin Hajji.   Bangarorin da ya kamata ya mayar da hankali   A karkashin jagorancin Farfesa Pakistan, ana sa ran samun ingantuwar tsari da aiwatar da ayyukan Hajji. Muhimman wuraren da ake sa ran jagorac insa za i   ba da fifiko sun hada da:   1. Inganta Jin Dadin Alhazai: Tabbatar da lafiya da walwala da jin dadin Alhazan Najeriya a lokacin tafiyar Hajji shi ne abu mafi muhimmanci. Wannan ya haɗa da samar da   mafi kyawun masauki, ingantaccen sufuri zuwa wurare masu tsarki, da s...

NAHCON Chairman Professor Pakistan's Leadership: Key Focus Areas, Challenges and Hopes for Nigeria's Hajj Management

Image
By Nura Ahmad Dakata The recent appointment of Professor Abdallahi Saleh Usman Pakistan as the Chairman of the National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) has sparks discussions on the future direction of Hajj management in Nigeria. As he will soon assumes leadership, several key areas of focus, potential challenges, and hopes for achieving the set goals have been identified by stakeholders in the Hajj industry.   Key Focus Areas Under Professor Pakistan’s leadership, there are high expectations for improvements in the organization and execution of Hajj operations. Key areas that his administration is expected to prioritize include:   Improved Pilgrim Welfare: Ensuring the safety, comfort, and well-being of Nigerian pilgrims during the Hajj journey is paramount. This includes better accommodation, efficient transportation to Holy sites, and access to healthcare services.   Streamlined Visa and Travel Processes: Addressing delays and complications in visa issu...

An Bukaci Shugaban NAHCON Ya Bada fifikon Kawo Sauyi da Tabbatar Da Tsantsaini

Image
  Sabon shugaban hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullah Saleh, ya samu sakon taya murna daga hukumar gudanarwar ta (Nigeria Hajj and Umrah Special Info) inda suka bayyana kwarin gwuiwarsu cewar Pakistan na iya jagorantar hukumar ta hanyar gaskiya da rikon amana.   A cikin sakon, kungiyar ta taya Farfesa Saleh Pakistan murna   kan nadin da aka yi masa, inda ta bayyana shi a matsayin wani gagarumin nauyi da ke zuwa a wani lokaci mai muhimmanci ga hukumar. Sanarwar ta bayyana kalubalen da magabacinsa ya fuskanta da suka hada da zargin cin hanci da rashawa, sannan ta jaddada muhimmancin maido da amana a cikin hukumar ta NAHCON.   Shugabannin gudanarwar kuniyar sun shawarci Farfesa Abdallahi Pakistan da ya ba da fifiko wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a dukkan ayyuka, inda suka bayar da shawarar samar da ingantacciyar hanyar sa ido domin kare kai daga cin hanci da rashawa da kuma kara sahihancin hukumar. Don tabbatar da jagoranci mai in...

Shugaba Tinubu Ya Nada Farfesa Pakistan A Matsayin Shugaban Hukumar NAHCON

Image
Shugaba Bola Tinubu ya nada Farfesa Abdullahi Saleh Usman  a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), inda ya sauke shugaban da ya gabata, Jalal Arabi, bisa zargin cin hanci da rashawa.  Farfesa Pakistan fitaccen malami ne da ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Madina da Jami’ar Peshawar da ke Pakistan.  A baya ya taba rike mukamin Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kano, inda ya samu nasarar kula da ayyukan mafi yawan alhazan kasar nan.   A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngalale ya fitar, majalisar dattawa ta tabbatar da nadin. “Shugaban kasa yana sa ran sabon shugaban NAHCON ya yi aikinsa bisa gaskiya, da rikon amana ga kasa,” in ji sanarwar.  Wannan ci gaban dai na zuwa ne bayan da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gurfanar da tsohon Shugaban Hukumar, Jalal Arabi, da Sakataren Hukumar, Abdullahi Kontagora bisa zargin karkatar da wasu sassan N90bn da Gwamnatin Tarayya ta fitar don tallafawa...

Bauchi Hajj Camp, Unstoppable Among More- NAHCON Head

Image
The chairman of National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) Alhaji Jalal Ahmad Arabi has described Bauchi ultra-modern Sultan Saad Abubakar Hajj Camp constructed by the State Government led by Governor Bala Mohammed as unbeatable among other camps across the Nigerian federation. Arabi was speaking when he paid an unscheduled visit to the Sultan Sa’ad Abubakar Ultra Modern Hajji Transit Camp in Bauchi yesterday in order to see for himself the nature of the edifice.  He acknowledged the contribution of Governor Bala Abdulkadir Muhammad towards the well being of intending pilgrims, also describing it as one of the best in the country.  On the 2024 hajj exercise, the NAHCON boss also called on states pilgrims welfare board whose pilgrims are yet to be flown to Saudi Arabia for this year’s pilgrimage to ensure speedy bringing them out to the designated airports for their journey to the Holy Land. The Chief Executive Officer of NAHCON who made the plea said, “We wish th...

Avoid Smuggling Prohibited Items into Saudi Arabia: NAHCON Warns

Image
Intending pilgrims for the 2024 Hajj are cautioned to refrain from travelling with illicit drugs, kola nuts, cigarettes etc., into the Kingdom of Saudi Arabia. The pilgrims are reminded that as a nation deeply rooted in religious and cultural heritage, Saudi Arabia holds strict laws against drug trafficking, penalty for which is death.   In a statement signed by the Assistant Director Public Affairs of the Commission, Fatima Sanda Usara, said NAHCON wishes to remind the pilgrims that the purpose of their trip to Saudi Arabia is for worship, therefore they should not be distracted by acts that would violate sanctity of their Hajj. Hajj period is a time for spiritual reflection and prayers that should be approached with reverence and respect for the laws and customs of the host country.   One the other hand, Commission’s management warns intending pilgrims to beware of being used as conduit for any illicit trade without their knowledge. Therefore, they are advised be...

Hajj 2024: Over Four Thousand Nigerian Pilgrims Arrives Makkah - NAHCON

Image
The National Hajj Commission of Nigeria, NAHCON, has confirmed that as at Tuesday this week, about five thousand Nigerian pilgrims have arrived the holy City of Makkah, after their four day stay in the holy Prophet City of Madinah.  The pilgrims were made up of those from Kebbi, Nasarawa States and the Federal Capital Territory, Abuja who were the first to arrive in the Kingdom of Saudi Arabia for this year's Hajj operation that started last week. The NAHCON Makkah Coordinator, Dr. Aliyu Abubakar Tanko disclosed this to Freedom Radio Group, Kaduna Station from Makkah. The Coordinator, who said that all the pilgrims that have arrived were hearty, healthy and all and about without stress, as most of them performed the lesser Hajj and now are only waiting for the actual greater annual religious event, which is expected to commence in next three weeks. Dr. Aliyu Tanko stated that as usual all necessary infrastructure and measures have been put in place to ensure peace, harm...

NAHCON: 2024 Hajj Airlift Enters Seventh Day

Image
By the end of 20th May 2024 being Day 6 of 2024 airlift, FlyNas has transported 4,665 pilgrims followed by Max Air with 4,479. Air Peace has so far conveyed 1,531 pilgrims within the six days of operations making a combined total of 10,675 pilgrims that have been flown to the Kingdom as at 20th of May.  Thus far, no flight cancellation has been recorded except for a flight delay that resulted in a time shift that affected the Kwara inaugural flight; moving it from yesterday 20th May, 2024 to early hours of today Tuesday 21st May.  Delightedly, Nasarawa state is the first to conclude airlift of its pilgrims totaling 1,794 for the 2024 Hajj season. Oyo and Armed forces are expected to conclude conveyance of their pilgrims tonight with one leg each remaining. As we approach the second week of inbound flights into Saudi Arabia, states that are about to commence airlifting of their pilgrims include Kaduna, Yobe, Kano, Adamawa, Borno, and Sokoto states. Plateau state pil...

Jami’an NAHCON Dake Makkah Sun Shirya Karbar Alhazan Da Suka Gama Zamansu Na Madinah

Image
Jami’an NAHCON sun shirya tsap don Tarbar Maniyyatan da suka kammala kwanakinsu hudu a Madinah.  A yayin da hakan ya tabbata ne saboda yadda Jami’an suka hada karfi da karfe tsakanin maaikatan NAHCON dake Makkah da wadanda ke Madinah wajen seta duk bukatun da Alhazan ke da Su a Makkah da suka shafi masaukai da wajajen dafa abinci.  A zagayen rangadin da Jami’an suka kai wajen dafa girkin da masaukan Alhazan da anjumar yau dinnan ne za su fara baro Madinah don shigowa Makkah bayan kammala kwanakinsu hudu a Madinah din, kampanonin dake dafa abinci sun tabbatarwa NAHCON za su ciyar da Alhazan ba tare da kwange ba hakazalika masu bada masaukai.  Hakan kuma yasa NAHCON ta sake jaddada lallai idan ba a bai Alhazanta abunda yarjejeniyar da suka rattabawa hannu ba to kampanonin su kwana da sanin za a ma iya soke kwangilar take-yanke.  Zuwa wani lokaci Kadan yau din  ne za a tabbatar da sa idon Jami’an NAHCON zai sa kampanonin bada hid...

Hajj2024: NAHCON Ta Tura Tawagar Farko Zuwa Saudia

Image
A gobe ne Tawagar Jami'an Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) su 43 za su tashi daga Abuja zuwa kasar Saudia domin fara gudanar da aikin Hajin bana  A sanarwar da mataimakin daraktan yada yada da dab'i na hukumar, Mousa Ubandawaki, yace Tawagar da ta kunshi Jami’an Hukumar NAHCON 35 da Ma’aikatan Lafiya 8 za su je kasar Saudiyya domin shirin karshe na karbar Alhazan Najeriya daga Jihar Kebbi da za su isa Masarautar a ranar Laraba 15 ga watan Mayu domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.  Da yake jawabi ga tawagar a wani dan takaitaccen biki na bankwana da aka gudanar a dakin taro na hukumar, Shugaban Hukumar Malam Jalal Ahmad Arabi ya taya tawagar murna da zaben da aka yi musu, sannan ya bukace su da su yi rayuwa mai kyau ta hanyar gudanar da ayyukansu kamar yadda aka umarce su. Don haka dole ne ku tashi tsaye domin samun ladan mu anan da na Allah a Lahira na kyautatawa baqonsa. Su ne dalilin da ya sa kuke wurin, don haka a kowane lokaci ku tabbatar da...

Hukumar Alhazai Jahar Kano Ta Biya Sama Da Naira Biliyan 18 Ga NAHCON Domin Hajin Bana

Image
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana a yau cewa hukumar ta aikawa hukumar alhazai ta kasa sama da Naira biliyan 18 domin shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin shekarar 2024.  A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa duk da cewa mutane 3,110 ne suka biya kudin aikin hajji, amma da yawa suna jiran bizarsu daga hukumar alhazai ta kasa.  Ya kuma bukaci hukumar da ta hanzarta bayar da bizar kafin rufe ranar, inda ya jaddada kudirin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na kammala gyara a sansanin Alhazai kafin a fara jigilar maniyyata.  Darakta Janar din ya kara da cewa, ba kamar shekarar da ta gabata ba, a  wannan shekarar gwamnati ta samar da dukkan kayayyakin da ake bukata a sansanin Alhazai  gabanin gudanar da aikin hajji domin amfanin Maniyyata ...

Shugaban NAHCON Ya Yabawa Gwamnan Imo Bisa Tallafawa Maniyyatan Jahar

Image
Hukumar alhazai ta kasa NAHCON a yau ta karbi bakuncin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda ya kai ziyarar ban girma a gidan alhazai dake Abuja. A sanarwar da mataimakin daraktan yada labarai na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace A jawabinsa na maraba, Malam Jalal Ahmad Arabi ya bayyana jin dadinsa da karbar bakuncin Gwamnan Jihar Imo a gidan Hajji. Arabi ya bayyana Gwamna Uzodinma a matsayin wani ginshikin tallafi ga Hukumar tare da bayyana yadda ya yi kokarin ganin alhazan jihar sa da ke da niyyar shiga aikin Hajjin bana. A cewarsa, “Kun kasance ginshikin goyon bayanmu a Hukumar ta hanyar goyon bayanku na ganin cewa Musulmin Jihar Imo sun samu damar shiga aikin Hajji. Kun tallafa mana a 2023 da ma bana duk da kasancewar kiristanci ne kuma jihar Imo jihar ce mafi rinjayen Kirista. A gare mu ku alama ce ta zaman lafiya tare da addini da hadin kai a kasar." Ya kuma baiwa Gwamna Hope Uzodinma takardar yabo da lambar yabo ta 🥈 f nagari bisa goyon bayansa...

NAHCON Ta Bukaci Hukumomin Alhazai Su Mika Mata Rukunin Maniyyatansu Kafin Ranar Juma'a

Image
Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) na fatan baiwa hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi da Hukumomi da Hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi da su kammala hada-hadar maniyyata zuwa kungiyoyi 45 domin kammala sanya bayanansu a yanar gizo daga nan zuwa Juma’a 26 ga Watan 2024. A sanarwar da mataimakin daraktan yada labarai na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace Waɗannan ƙungiyoyin an yi su ne don sauƙi na bayar da biza a kan dandalin e-track na Visa na Saudiyya. Haka kuma ya yi daidai da manufofin Saudiyya na tilas a kan tara Tafweej don tafiyar Hajjin 2024. Idan dai za a iya tunawa, Masarautar Saudiyya ta bullo da sabbin matakan gudanar da ayyukan Hajjin bana, daya daga cikinsu shi ne na wajabta tara maniyyata zuwa kungiyoyi 45. Don haka, takardar bizar Mahajjata za ta ba da biza ne kawai idan sun kammala rukuni na 45.   Haka kuma, NAHCON tana jan hankalin duk maniyyatan da ke son tafiya tare a rukunonin da ake bukata, da su hadu da hukumomin jin dadin Alhazai...

Zamu Iya Mayarwa Da Maniyyata RararKudi Saboda Karyewar Dala- NAHCON

Image
Shugaban hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Jalal Ahmad Arabi ya ce akwai yiwuwar hukumar ka iya mayar wa maniyyata rarar kuɗin da suka biya sakamakon karyewar farashin dalar Amurka. Alhaji Jalal Arabi ya shaida hakan ne a wata hira da kafar sadarwa ta DCL da ke intanet wadda kuma hukumar alhazan Najeriya ta wallafa a shafinta na X, ranar Alhamis. "Idan misali ranar da muka yi shela dala tana naira 1000, sai ya zamana kai ranar da ka saka kuinka ka saka ne ranar da take naira 900, to ai ka ga akwai ranar naira 100. Wannan naira 100 ya kamata ma mu maida maka. Ba mu jira tana ta yin asa ba. To idan kuma ta ara yin sama fa?" In ji Jalal Arabi. Ya ara da cewa "indai da rai da lafiya kuma idan dai mu ne a kan kujerar to ba za mu zauna a kan hakkin kowa ba da iznin Allah. Za mu tabbatar mun biya wannan rarar." To sai dai shugaban hukumar ta Alhazan na Najeriya ba faɗi lokacin da za a mayar wa da maniyyatan rarar kuɗaɗen nasu ba. A mafi yawancin lokuta dai hukum...