Duk Mai Son Mukami A Gwamnanatina Sai Ya Kawo Akwatinsa Lokacin Zabe - Atiku
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce duk dan jam’iyyar da ke neman kwagila ko mukami a gwamnatinsa, sai ya nuna sakamakon zaben mazabarsa kafin a ba shi. Atiku ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abekuta babban birnin Jihar Ogun, yayin taron ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar. Atiku ya ce halartar kowanne yakin neman zaben jam’iyyar ba shi ne tabbacin samun matsayi ko kwangila a gwamnatinsa ba, jajircewa wajen ganin an kawo akwatinan mazaba ne. Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya kuma ce, “Dukkanku magoya bayan PDP ne, kuma kuna so ta dawo mulki, don haka ina rokonku ku tabbatar kun kawo akwatinan mazabunku. Yawon zuwa yakin neman zaben kafatanin ’yan takarar jam’iyya ba shi ne zai sa ka samu aiki ko matsayi ko kwangila ba idan an ci zabe, hanyar da kadai za ku samu shi ne nuna min sakamakon zaben mazabarku. “Kuma ina bai wa kowanne dan takarar PDP umarnin yin hakan, domin da haka ne kadai za mu ci zabe. Atiku ya kuma yi alkawarin farfado ...