Gwamna Ganduje ya bayyana Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin Mutum mai Biyayya da Amana

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan a yayin taron yakin neman zaben jam'iyyar APC a kananan hukumomin Sumaila da Takai.

Ya kuma bukaci al’ummar kananan hukumomin biyu da su zabi dan takarar gwamna na jam’iyyar APC da abokin takararsa domin dukkansu an gwada su kuma an amince da su.

Gwamnan ya bayyana cewa su biyun sun cancanci a zabe su saboda irin nasarorin da suka samu a ma’aikatun gwamnati daban-daban da suka yi aiki a tsawon shekaru.

Dakta Ganduje ya yi nuni da cewa Dr. Nasiru Yusuf Gawauna da Alhaji Murtala Garo sun cancanta haka kuma su sukafi da cewa su gajeshi domin ci gaba da ayyuka da shirye-shiryen gwamnati a bangarori daban-daban da Gina dan Adam.

Ya kuma bayyana fatansa na cewa ‘yan takarar na da kwarewa wajen fito da manufofi da shirye shirye da kuma aiwatar da karin manufofi da tsare-tsare da suka shafi ci gaban jihar, idan har aka ba su wa’adi a babban zabe mai zuwa.

Gwamnan ya yi amfani da damar wajen yin kira ga masu zabe da su kada kuri’ar su ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Sanata Asiwaju Bola Ahmad Tinubu inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai rikon amana, mai dattako da kwarewa don kai Najeriya mataki na gaba.

A nasa bangaren mataimakin gwamnan jihar wanda kuma shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr Nasiru Yusuf Gawauna, ya bayyana cewa daga dukkan alamu za a zabi shi da abokin takararsa a matsayin gwamna da mataimakin gwamna idan Allah ya yarda.

Ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su zabi jam’iyya mai mulki a lokacin zaben Gwamna da ke karatiwa, inda ya yi alkawarin aiwatar da kuduririn da ya alkarwanta.

Tun da farko, shugaban jam’iyyar APC na jiha Alhaji Abdullahi Abbas, ya ce yawan jama’ar da suka halarci taron gangamin yakin Neman zaben shaida ce a fili cewa jam’iyyar APC ce za ta lashe dukkan mukamai a zabe mai zuwa.

Daga cikin abubuwan da aka gudanar a wajen taron ya hada da mika tutar jam'iyyar APC ga Dan takarar majalisar wakilai ta tarayya da na majalisar dokokin jiha na yankin.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki