Game Da Tafiya A Motar Haya Kashi Na 3 - Dr Dukawa
HALIN DA WASU TASHOSHIN MOTA SUKE CIKI A bisa kiyasi, tashar Na’ibawa a Kano ba za ta gaza shekara arba’in (40) ba. Saboda an samar da ita ne a zamanin marigayi gwamnan tsohuwar jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi (1979 – 1983). Amman har izuwa yau tashar tananan jiya ya yau: kango wanda babu wani abu da yake nuna ana samun kudi a wurin; babu kwalta, babu interlocks, babu dabe kowane iri! Zaiyar kasa. Sai yalwar leda da sauran nau’i na shara. Babu wani lafiyayyen makewayi. Da na bukaci wurin yin bawali sai aka nuna min wani uban juji a yammacin cikin tashar. Sai da roki wani dan bola jari cewar ya dan kauce zan kama ruwa. Na tabbatar idan ruwa ya sauka mummunan halin da tashar ke ciki ba zai gaza na tashar Unguwa Uku ta Kano ba, wacce na yi rubutu akan nata halin da take ciki a sherarar 2020. An yayyanka pilotai a cikin tashar Na’ibawa. Wasu an gina shaguna ana gudanar da ciniki wasu kuma an saka fandisho na gini ba a yi ginin ba. Babu Masallaci sai ‘yar musall...