Zanga-Zanga : Gwamna Abba Kabir ya Gana Da Shugabannin Al'uma
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gana da wakilan al'umma wadanda suka fito daga bangarori daban-daban na rayuwa, yayin da ake shirin gudanar da zanga-zangar da za a yi ranar Alhamis 1 ga watan Agusta, 2024. Mahalarta taron sun hada da: sarakunan gargajiya, Malamai, ‘yan kasuwa, malamai, shugabannin masana’antu da kungiyoyin mata. Da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a wajen taron, Gwamna Abba Kabir ya ce an yi taron ne domin a tattauna sosai da nufin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kawo wa al’ummar jihar karshen abubuwan dake ci musu tuwo a kwarya. Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai. Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa mutane na da ‘yancin yin zanga-zanga a tsarin mulki, amma duk da haka ya kamata a kasance cikin lumana ba tare da yin wani abu da zai iya haifar da tarzoma ko barazana ga rayuka da dukiyoyi ba. Ya kuma umurci wadanda suka shirya zanga-zangar da ba a san...