Search This Blog

Showing posts with label CBN. Show all posts
Showing posts with label CBN. Show all posts

Thursday, 11 January 2024

CBN Ya Nada Sabbin Shugabannin Bankunan Union, Keystone Da Polaris

Sabbnin nada-naden sun fara aiki ne nan take


Babban Bankin Najeriya (CBN) ya nada sabbin shugabannin bankunan Union da Keystone da Polaris.

CBN ya nada sabbin shugabanni da manyan daraktocin bakunan ne sa’o’i kadan bayan ya sanar da rushe majalisar daraktoci da kwimitin gudanarwan bankunan.

Da take sanar da hakan a safiyar Alhamis, Daraktar yada labaran CBN, Hakama Sidi Ali, ta ce sabbin nade-naden sun fara aiki ne nan take.

Hakama Sidi Ali ta ce CBN ya nada Yetunde Oni a matsayin sabuwar Manajan Darakta kuma Shugabar Bankin Union, Mannir Ubali Ringim kuma Babban Daraktan Gudunarwa na bankin.

Bankin Keystone kuma, Hassan Imam shi ne sabon Manajan Darakta kuma Shugaba, tare da Chioma Mang a matsayin Babban Daraktan Gudunarwa.

A Bakin Polaris kuma, Lawal Mudathir Omokayode Akintola ne sabon shugaba kuma Manajan Darakta, Daraktan Gudunarwansa kuma Chris Ofikulu.

Babban Bankin ya sanar da sabbin nade-naden a ranar Alhamis ne washegarin da ya rushe kwamitocin daraktocin bankunan kasuwancin.
(AMINIYA)

Friday, 15 September 2023

Da dumi-dumi: Tinubu ya nada sabon gwamnan CBN da 'yan tawagar gudanarwa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Dr. Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da yada labarai Ajuri Ngelale a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, da farko Dr. Cardoso zai yi wa’adin shekaru biyar, yana jiran amincewar majalisar dattawan Najeriya.

Wannan shawarar ta yi dai-dai da sashe na 8 (1) na dokar babban bankin Najeriya na shekarar 2007, wanda ya baiwa shugaban kasar Najeriya ikon nada gwamna da mataimakan gwamnoni hudu a CBN, idan har majalisar dattawa ta tabbatar da hakan.

Bugu da kari, shugaba Bola Tinubu ya kuma bayar da nadin nasa nadin nadin sabbin mataimakan gwamnoni hudu na CBN. Su ma za su yi wa’adin farko na shekaru biyar, har sai majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da hakan.

Sunayen wadanda aka nada sune kamar haka.

(1) Mrs. Emem Nnana Usoro

(2) Malam Muhammad Sani Abdullahi Dattijo

(3) Malam Philip Ikeazor

(4) Dr. Bala M. Bello

“A bisa tsarin sabunta bege na shugaban kasa Bola Tinubu, shugaban kasar na fatan wadanda aka zaba a sama za su samu nasarar aiwatar da muhimman gyare-gyare a babban bankin Najeriya, wanda zai kara kwarin gwiwar ‘yan Najeriya da abokan huldar kasa da kasa wajen sake fasalin tattalin arzikin Najeriya don samun ci gaba mai dorewa. da wadata ga kowa da kowa,” in ji Ngelale.

Thursday, 25 May 2023

Bankuna Za Su Fara Ba Da Katin Dan Kasa Mai Hade Da Na ATM —Pantami

Gwamnatin Tarayya ta ba wa bankunan kasuwanci izinin fara ba wa abokan huldarsu katin cirar kudi na ATM da ke hade da katin shaidar dan kasa a wurin guda.

Ministan Sadarwa mai barin gado, Isa Ali Pantami, ya sanar cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince bankuna su fara bayar da katin na bai-daya ba tare da sun caji kwastomomi ko sisi a kan kudin katin ATM da aka saba ba.

“An ba wa bankuna izinin buga katunan Mastercard ko Visa da za su yi amfani a matsayin katin shaidar dan kasa ba tare da sun caji ’yan Najeriya karin kudi ba.

“Duk mai son karbar katin banki, sai ya sanar da su cewa mai hade da katin dan kasa yake so, sai su ba shi kati daya da ya hade abubuwa biyun,” in ji Pantami.
Ya bayyana cewa, Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) ta yi haka ne da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) “domin saukaka wa duk mai bukata samun katin dan kasa ta hannun bankinsa.”

Da yake jawabi bayan zaman karshe na Majalisar Zartarwa ta Tarayya da gwamnatin Buhari ta gudanar, a Fadar a Shugaban Kasa ministan, Pantami ya bayyana cewa Dokar NIMC ta 2007, ta wajabta wa ’yan Najeriya mallakar lambar shaidar dan kasa (NIN) ne kawai.

Ya ci gaba da cewa, “A lokacin mallakar katin shaidar ba dole ba ne, ra’ayi ne; Amma sai mutane suka rika kai wa NIMC korafi cewa ba su samu katinsu na dan kasa ba.

“A kan haka ne a shekarar 2022 muka fito da katin shaidar dan kasa na zamani, wanda mutun zai iya saukewa a wayarsa, wanda kuma ke amfani ba lallai sai mutum ya buga shi a takarda ba.

“Duk da haka aka ci gaba da samun korafi, musamman daga mazauna yankunan karkara, cewa suna bukatar rike katinsu na dan kasa a hannu.

“Shi ya sa muka saukaka samun katin, inda NIMC da bankin CBN suka yi hadin gwiwa domin tabbatar da ganin mutane za su iya zuwa bankunansu su karbi katin dan kasa mai hade da ATM.”
Sai dai bai fayyace lokacin da bankunan za su fara bayar da katin na bai-daya ba.

Idan za a iya tunawa a baya CBN ya sanar da shirinsa na bullo da katin cirar kudi a banki na bai-daya, wanda mutum zai iya cirar kudi daga asusun ajiyarsa da ke bankuna daban-daban.
AMINIYA 

Thursday, 16 March 2023

Sai Buhari Ya Yi Magana Za Mu Karbi Tsohon Kudi —’Yan Kasuwa


 ’Yan kasuwa a wasu yankunan Najeriya sun bayyana cewa ba za su fara karbar tsoffin takardun N5oo da N1,000 har sai sun ji Shugaban Kasa Muhamamdu da bakinsa ya ce su fara karba.

’Yan kasuwa da kwastomominsu jihohin Kaduna da Legas da kananan hukumomin Abaji da Kwali a Yakin Babban Birnin Tarayya na kin karbar tsoffin kudin ne, a washgarin da bankunan kasuwanci suka fara bayar da su, bisa umarnin Babban Bankin Najeriya (CBN).

Sai dai a Jihar Kano, harkokin kasuwanci sun fara komawa yadda aka saba, tun bayan da bankuna suka fara bayar da tsoffin kudi, kuma mutane suka ci gaba da amfani da su a harkokin kasuwanci.

Harkoki sun fara kankama a Kano

Wani tan kasuwa a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, Adamu Hamza, ya ce sun fara samun karuwar ciniki,  “tsakanin jiya (Talata) da yau (Laraba), kudi ya fara yawo a hannun jama’a, suna kawowa kuma muna karba.”

Aminiya ta ruwaito cewa tun ranar Talata injinan ATM a birnin Kano suka fara bayar da tsoffin kudin, sai dai yawanci N500 ne.

Haka kuma an samu raguwa mutane da ke neman cirar kudi, dai dai wasu bankunan sun bayyana cewa tsabar kudin da ke hannunsu  ya kare, shi ya sa ba a ganin layin mutane a ATM dinsu domin cirar kudi.

‘Sai mun ji daga bakin Buhari’

Aminiya ta zaiyarci yankin Abaji a ranar Laraba, inda ta iske mutane na ta gunaguni cewa bankuna sun koma ba wa mutane tsoffin takardun kudin.

Wani dan kasuwa, Bashir Aliyu, ya yi mana korafin cewa ya ce cikin banki cirar kudi , amma aka ba shi tsoffin takardun N1,000 da aka sauya, amma ya ki karba, sabo ba zai iya kashe su cikin sauki ba, idan ya je kasuwannin kauye.

A cewarsa, duk da cewa CBN ya ba umarnin bankuna su ci gaba da harkokinsu da tsoffin kudin, shi ba zai samu natsuwa ba sai sai ya ji Shugaba Buhari da kansa ya yi wa ’yan kasa magana cewa su ci gaba da amfani da tsoffin kudin.

Wani jami’in banki da ya nemi mu boye sunansa ya shaida mana cewa bankin ya fito da Naira dubu 500 na tsoffin takardun kudi da yake da su domin ba wa mutanen da suka zo cirar kudi, amma yawancin mutanen sun ki karba.

“A takaice, daga cikin N500,000 da bankin ya fitar domin ba wa kwastomomi N150,000 kadai aka samu wadanda karba,” in ji jami’in bankin.

Hakazalika wasu ’yan kasuwa a yankin Kwali na kin karbar tsoffin kudin, saboda har yanzu ba su ji Shugaba Buhari ya yi magana a kai ba.

Wata ’yar kasuwa mai suna Misis Laraba Gwatana ta ce, “Ni ba zan karbi tsohon kudi ba, saboda har yanzu rade-radi muke ji cewa CBN ya umarci bankuna su koma bayar da tsoffin kudaden.

“Amma ni dai ba zan karbe su ba, sai lokacin da na ji Buhari ya fito ya yi wa ’yan Najeriya jawabi cewa su rika karbar tsoffin kudin; gaskiya ba wanda ke so ya kara yin asara.”

’Yan kasuwa kaduna ma haka

Zuwa ranar Laraba, ’yan kasuwa da dama a Jihar Kaduna na kin karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 a Kasuwar Sheikh Gumi, inda suke bayyana fargaba kan batun amfani da tsoffin kudaden.

Wakilinmu ya lura cewa maimakon karbar tsoffin kudaden, ’yan kasuwa da dama sun tanadi na’uarar tura kudi ta PoS ga kwastomominsu.

Wani dan kasuwa mai sayar da kayan gwari, Malam Lawal Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa, “ban fara karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 tukuna; amma ina karbar tsohuwar N200.”

Ya ce dalilinsa shi ne, “Gwamnati na ta kumbiya-kumbiya, don haka ina tsoron in karba, daga baya CBN ya ce ya canza shawara a bar ne da asarar biyan kudin kaya, shi ya sa ba na karba.”

Mohammed Isa mai kayan gwari shi ma ya ce, gara ya ki karbar tsoffin kudaden da ya bari su ja masa asara.

“Lokacin da aka fara cewa mu kai tsoffin kudin CBN, sai da na yi kwanaki a kofar CBN don in ajiye N100,000. Shi ya sa na yi wa kaina riga-kafi, da in yi asara gara kaya na sun yi kwantai.”

Yankin Kudu

Wannan yanayi haka yake a wasu sassa na Jihar Legas, inda bakuna suka fara bayar da tsoffin kudin, amma na dar-dar wajen yin cinikayya da su, duk kuwa da umarnin CBN na ci gaba da amfani da su zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

A Jihar Ribas kumma, manyan shaguna da gidajen mai da wasu wuraren kasuwanci na ci gaba da harkokinsu da tsoffin kudin.

Sai dai an korafi cewa duk da cewa bankuna na bayar da tsofifn kudaden, amma idan aka kai musu ba sa amsa.

Wata mazauniyar garin Fatakwal, Amaka Ike, wadda wakilinmu ya zanta da shi ya ce, ta ce da kyar ta iya yin sayayya da tsofifn kudaden.

Amaka ta ce, “wasu masu shaguna, gidajen mai da wasu ’yan kasuwa ba sa karbar tsoffin kudaden saboda a cewarsu, har yanzu ba su natsu ba, gwamnati za ta iya sauya shawara a kowane lokaci, kan batun.”

AMINIYA

Tuesday, 21 February 2023

Bankin CBN Ya ce Har Yau Yana Nan Kan Bin Umarnin Shugaba Buhari Na Ci Gaba Da Amafani Da Tsofaffin Kudi Na 200 Kadai

Friday, 17 February 2023

Yadda CBN Ya Lashe Amansa Kan Karbar Tsoffin N500 Da N1,000

 


Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jefa ’yan Najeriya cikin rudani bayan ya fitar da sanarwa masu cin karo da juna kan ci gaba a karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 cikin dan kankanin lokaci.

CBN ya lashe amansa ne bayan manyan bankunan kasuwanci irinsu UBA da First Bank sun tura wa abokan huldarsu sakonni cewa za su ci gaba da karbar tsoffin takardun N500 da N1,000.

Bankunan sun yi haka ne bayan wata sanarwar da kakakin CBN, Osita Nwanisobi, da ke umartar su da karbar kudin matukar ba su wuce N500,000 ba.

Sakonsa ga  bankunan ya ce,

“Kwastoma zai iya kai har N500,000 bankin kasuwanci, amma abin da ya haura hakan sai dai ya kai ofishin CBN.

“Don haka ana bukatar ku bi wannan umarnin,” in ji wasikar farko da babban bankin ya aike wa manajojin reshe da ayyukan bankunan kasuwancin.

Bayan fitowar wasikar, ’yan jarida sun tuntubi Mista Nwanisobi, game da ita, wanda ya tabbatar musu da sahihancinta.

“Duk wanda ke da tsoffin takardun kudin da suka haura N500,000 ya kai ofishin CBN mafi kusa

“Muna kuma sanar da ku cewa za mu bude rassanmu gobe Asabar 18 ga Fabrairu, 2023.”

Shi ma bankin UBA ya tura irin wannan sako ga kwastomominsa kamar haka: “Ba mu daina amsar tsoffin takardun N500 da N1,000 ba, matukar ba su haura N500,000 ba.

Bankunan sun tura sakonnin ne a ranar Juma’a.

Amma kafin a jima, bayan kafofin watsa labarai su wallafa labarin, sai CBN ya fitar da wata sabuwar sanarwa, yana karyata umarninsa na farko da ya baiwa bankuna su ci gaba da karbar tsofaffin N500 da N1000.

A sabuwar sanarwar, kakakin na CBN ya zargi kafofin watsa labarai da yada labarin karya — wato sanarwarsa ta farko wadda shi da kansa ya tabbatar musu da sahihancinta.

“ To a sani cewa, kamar yadda Shugaban Kasa ya ba da umarni, tsoffin takardun kudi da za a ci gaba da amfani da su, su ne N200 na tsawon kwana 60 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.”

A kan haka ne First Bank ya goge sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Wannan dambarwar ta zo ne washegarin jawabin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ya ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira 200 tare da sabbin takardun Naira 200, 500 da kuma 1,000 har zuwa 10 ga watan Afrilu, ranar da tsohuwar 200 za ta daina aiki.

Buhari ya sanar da haka ne a jawabinsa ga ’yan Najeriya da ke ci gaba da surutu kan sauyin takardun kudin da CBN ya yi, da kuma karancin sabbin da ya jefa su cikin damuwa.

Hannu guda kuma gwamnatocin was jihohi sun maka Gwamnatin Tarayya a Kotun Koli suna neman ta soke dokar haramta amfani da tsoffin kudin.

Batun karancin sabbin takardun kudin dai ya jefa ’yan Najeriya cikin kunci, har da asarar rayuka.

A wasu jihohin Kudu abin ya kai ga tarzoma da kona bankuna.

AMINIYA

Babban bankin Najeriya (CBN) ya musanta rahotannin da ake ta yadawa cewa ya ba bankunan ajiya izinin karbar tsoffin takardun kudi na N500 da N1,000.

A wata sanarwa da Osita Nwanisobi, Daraktan Sadarwa na Babban Bankin na CBN ya fitar a ranar Juma’a, babban bankin ya ce don kaucewa shakku ne kawai CBN ke sake fitar da wasu tsofaffin takardun kudi na Naira 200 kuma ana sa ran za a rika yawo a matsayin takardar kudi na tsawon kwanaki 60 har zuwa watan Afrilu. 10, 2023, daidai da shirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kasa ranar Alhamis.


Babban bankin na CBN ya shawarci jama’a da su yi watsi da duk wani sako da/ko bayanan da bankin bai fitar a hukumance ba kan wannan batu.

Ta kuma shawarci masu aikin yada labarai da su yi kokarin tabbatar da duk wani bayani daga majiya mai kyau kafin a buga su.

Sanarwar ta kara da cewa;

An jawo hankalin babban bankin Najeriya kan wasu sakonni na bogi da ba da izini ba da ke ambato babban bankin na CBN na cewa ya ba bankunan ajiya izinin karbar tsoffin takardun kudi na N500 da N1,000.

Domin kaucewa shakku, kuma bisa tsarin yada labarai na shugaban kasa na ranar 16 ga Fabrairu, 2023, an umurci CBN da sake fitar da tsoffin takardun kudi na N200 KAWAI kuma ana sa ran za a yi ta yawo a matsayin takardar kudi na tsawon kwanaki 60 har zuwa 10 ga Afrilu. , 2023.


Don haka ya kamata jama’a su yi watsi da duk wani sako da/ko bayanan da babban bankin Najeriya bai fito a hukumance ba kan wannan batu.
DN24

Tuesday, 14 February 2023

Wa'adin Dena Karbar Tsofaffin Kudi Ya Cika - CBN

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya jadadda cewar ranar 10 ga watan Fabrairu ne wa’adin amfani tsofaffin takardun Naira ya cika.

Emefiele ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da jami’an diflomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Waje da ke Abuja a ranar Talata.

“Lamarin ya lafa sosai tun bayan lokacin da aka fara biyan kudi a kan kanta wanda hakan ya rage dogayen layuka a ATM.

“Don haka babu bukatar la’akari da wani sauyi daga wa’adin ranar 10 ga Fabrairu,” in ji shi.

‘Yan Najeriya sun shiga rudani yayin da bankunan kasuwanci suka daina karbar tsoffin takardun tun daga ranar Litinin.

Da yake karin haske, Emefiele ya ce, “Wasu daga cikin shugabanninmu suna siyan sabbin takardun kudi suna ajiyewa saboda wata manufa saboda haka ba zan iya yin karin haske kan hakan ba.”

Emefiele ya ce babban bankin ya san irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke sha sakamakon canjin kudin, amma ya ce tsarin zai iya kawar da kashi 4 cikin 100 na hauhawar farashin kayayyaki.

Ya kuma yi bayanin cewa kamata ya yi a ce adadin kudin da ke zagawa a hannun al’umma ya kai kusan Naira biliyan 700.


Ana iya tuna cewa, a bayan nan ne dai gwamnatocin jihohin Kaduna, Zamfara da Kogi suka maka CBN da Gwamnatin Tarayya a gaban Kotun Koli suna kalubalantar sabon tsarin amfani da sabbin takardun kudi. 

AMINIYA 


Wednesday, 8 February 2023

Kotun Ƙolin Ta Dakatar Da Gwamnatin Najeriya Dga Aiwatar Da Wa'adin Amfani Da Tsofaffin Kudi

Kotun Ƙolin Najeriya ta dakatar da gwamnatin tarayya daga aiwatar da wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin kasar.

A baya dai CBN ya saka 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin takardun naira 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sauya wa fasali.

Jihohin arewacin ƙasar uku, waɗanda suka haɗa da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da ƙarar a gaban Kotun Ƙolin ƙasar suna buƙatar kotun da ta hana Babban Bankin ƙasar aiwatar da wa'adin.

A hukuncin wucin-gadin da suka yanke, alƙalan kotun bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari'a John Okoro, sun dakatar da gwamnatin tarayya da Babban bankin ƙasar da sauran bankunan kasuwanci na ƙasar daga aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar.

Kotun ta kuma ce dole ne gwamnatin tarayya da CBN da kuma sauran bankunan ƙasar su jingine batun aiwatar da wa'adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin a ranar 15 ga watan Fabrairu.

Wannan hukunci na nufin a halin yanzu al'ummar Najeriya za su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin ƙasar har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukuncin ƙarshe.

Batun wa'adin amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar dai ya zama wani batu da ya ɗauki hankula a 'yan kwanakin nan.

Friday, 3 February 2023

Gwamnoni Sun Roki Buhari A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Kudi

 


Gwamnonin Jam’iyyar APC sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa baki a ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sabbin takardun kudi.

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne ya bayyana hakan bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa a Abuja.

Ya ce yayin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karbi sama da Naira tiriliyan biyu na tsofaffin kudi, amma iya Naira biliyan 300 kacal ya iya bugawa wanda a cewarsa hakan ba zai wadatar da mutane ba.

El-Rufai, wanda ya samu rakiyar takwaransa na Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kamata ya yi CBN ya buga akalla rabin abin da suka tara.

Ya ce gwamnonin jam’iyyar sun shaida wa shugaban kasa wawahalar da talakawa ke sha, da asar kayayyaki da ’yan kasuwa ke yi saboda rashin samun masu sayen kayansu.

Ya ba da misali da yadda masu sayar da tumatur suka je Legas da kayansu amma suka lalace saboda mutane ba su da kudin saye.

El-Rufai ya ce gwamnonin sun roki shugaban kasa da ya sake duba halin da ake ciki.

Ya kara da cewar shugaban gamayyar gwamnonin, Atiku Bagudu, ya sake ganawa da shugaban kasa shi kadai don jan hankalinsa kan bukatar janye dokar daina amfani da tsofaffin kudi.

A nasa bangaren, Gwamna Ganduje, ya ce shugaba Buhari ya yi alkawarin duba bukatarsu.

Friday, 27 January 2023

Sabon Kudi: Ganduje ya tausaya wa jama'a, ya kuma yi kira da a tsawaita wa'adi


Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jajanta wa al'ummar jihar kan wahalhalun da ake fama da su a sakamakon manufofin gwamnatin jihar. sabuwar manufar babban bankin Najeriya (CBN) kan sake fasalin kudin naira wanda ya fara yaduwa a makon jiya.

Kwamishanan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, ya ce gwamnati ba ta ji dadi ba matuka bisa ga sakamakon da aka samu na wannan manufa da ke shafar al'umma musamman talakawan Najeriya saboda lokacinta da kuma gajeren lokacin mika mulki.

Malam Garba ya bayyana cewa Gwamna Ganduje ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar na bakin kokarinta na hada kai da sauran masu ruwa da tsaki. duba da tsawaita wa'adin da aka sanya domin janye tsofaffin gaba daya tare da bayar da isassun kudade ga al'umma.

Kwamishinan ya kara da cewa, yayin da gwamnati, da mafi yawan 'yan Najeriya , sun yi imanin cewa jama’a na fuskantar wahalhalu sakamakon sake fasalin kudin Naira, ya kuma yi kira ga babban bankin CBN da ya kara wa’adin da aka sanya na aiwatar da manufofin.

Akan karancin man fetur da ake fama da shi, sanarwar ta kuma bukaci kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ) domin tabbatar da wadata da rarraba shi ga 'yan Najeriya.

Gwamnan ya bukaci jama'ar jihar da su kwantar da hankalinsu domin daukar matakin da ya dace domin gyara al'amura.

Friday, 20 January 2023

Wa’adin Tsofaffin Kudi: Mun Zuba Ido Mu Ga Yadda CBN Zai Kare Da Mutanen Karkara —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce Babban Bankin Najeriya (CBN) bai sanya su cikin masu ruwa da tsaki ba kan batun sauya fasalin takardun kudi, dalilin ke nan da suka zuba ido su ga yadda zai kare da mutanen karkara idan wa’adin karbar tsohuwar naira ya cika.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin Babban Jami’in Gudanarwa na CBN shiyyar Sakkwato, Dahiru Usman hadi da wasu jami’an babban bankin ranar Alhamis a fadarsa.

Alhaji Bako Zuntu ya riga mu gida gaskiya
Duk da gargadin CBN har yanzu bankuna na bai wa mutane tsohuwar naira ta na’urar ATM
Abubakar ya ce kamata ya yi a ce CBN din ya sanya dukkanin masu ruwa da tsaki tun a matakin farko na sauya takardun na naira, amma sai ya yi biris da sarakunan gargajiya.

“Akwai mutanen karkarar ma da ba su san an sauya kudin ba kwata-kwata, kuma idan ka ba su sabo ba za su karba ba saboda za su zaci na bogi ne.

“Mu ne muke kusa da su, mu ne kuma ke da hanyoyin isar musu da sakon, don bibiyar kafafen yada labarai ba dabi’ar mutanen karkara ba ce.

“Amma da muka ga ba a saka mu a lamarin ba, sai muka koma gefe mu ga yadda za a kare idan wa’adin karbar tsofaffin kudin ya cika.

“Duk da haka muna rokon CBN ya kara duba wa’adin da ya bayar, domin rashin tsaro na daga cikin dalilan da suka sa mazauna karkara ke tsoron dibar kudi masu yawa su kai bankuna, gudun yi musu fashi a hanya ko ma sace su gaba daya,” in ji shi.

A nasa bangaren, Babban Jami’in na CBN ya ce sun kawo ziyarar ce domin sanar da Sarkin a hukumance cewa an sauya takardun kudin, da kuma neman shawarwarinsa.

Ya kuma yi alkwarin isar da sakon Sarkin ga shalkwatar CBN din da zarar sun kammala zagayen duba yadda bankuna a jihar ke bayar da sababbin takardun kudin da suka je yi.

Monday, 16 January 2023

Hukumar DSS Ta Musunta Mamaye ofishin Gwaman Babban Bankin Najeriya


Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta mamaye harabar babban bankin Najeriya, a ranar Litinin, kamar yadda ake yada labarin a yanar gizo.

Rundunar ‘yan sandan sirrin a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaron ta farin kaya, Peter Afunanya ya fitar ta ce labarin karya ne.

Idan dai za a iya tunawa a ranar Litinin din da ta gabata ne aka ga motocin a harabar babban bankin da ke Abuja.

Hukumar ta DSS a cikin sanarwar ta ce jami’anta ba su yi yunkurin kama gwamnan na CBN ba.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Dala LGA Donates Building as Operational Base to Multi-Joint Task Force

In a show of unified resolve against drug abuse and related crimes, Dala Local Government has donated a local government–owned b...