Posts

Showing posts with the label Majalisar dattawan Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa majalisar dattawan Kano

Image
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa majalisar dattawan Kano (KEC) domin ta kasance mai ba da shawara ga gwamnatin jihar Kano. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Allah SWT ya albarkaci Kano da dimbin dattijai da tsofaffin shugabanni da suka kai ga kololuwar sana’o’insu kuma suka ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya. Majalisar Dattawa ta kunshi tsofaffin Gwamnoni, Mataimakan Gwamnoni, Shugabannin Majalisar Dattawa, Shugabannin Majalisar Wakilai, Shugabannin Majalisar Jiha, Mataimakan Shugaban Majalisar, Alkalan Kotun Koli da suka yi ritaya, Alkalan Kotun daukaka kara da suka yi ritaya, tsofaffin alkalan jihar, tsofaffin alkalai. Sakatarorin Gwamnatin Jiha, da Tsoffin Shugabannin Ma’aikatan Jiha, wadanda dukkansu ‘yan asalin jihar ne. Bugu da kari, majalisar ta hada da shugabannin Malamai, ‘yan kasuwa, sarakunan gargajiya, tsofaffin shuga