Posts

Showing posts with the label Hukumar Karbar Korafe Korafe

Batan Sama Da Naira Biliyan Hudu : Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano Ta Kama Babban Wanda Ake Zargi

Image
Inuwa, wanda shi ne wanda ya kafa kungiyar (Association of Compassionate Friends) kuma shi kadai ne ke sanya hannu kan asusun ajiyar wani kamfani mai suna Limestone processing Link da aka fi amfani da shi wajen karkatar da abin da aka gano. A sanarwar mai dauke da sa hannun mai bawa Shugaban Hukumar shawara kan harkokin yada labarai, Kabir Abba Kabir, tace an kama shi ne bayan da ya fasa rumfunan adana kayayyaki da aka kwace bisa ga sashe na 40 na Dokar Korafe-korafen Jama'a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta 2008 (kamar yadda aka gyara) wani mataki wanda kuma ya samu izini bisa umarnin kotu. An kama shi ne dangane da zargin karkatar da kudade da karkatar da kudade ko kuma mayar da kudaden gwamnatin jihar Kano na sama da naira biliyan hudu da aka tura wa tallafin kamfanin noma na Kano. Haka zalika, Bala Inuwa Muhammad wanda ya rattaba hannu a kai shi da mahaifinsa suka karkatar da kudaden da suka kai biliyan uku da miliyan dari biyu da saba’in da biyar da miliyan dari s...

Bayan Sanarwar Dawo Da Shi Kan Mukaminsa, Barista Muhuyi Magaji Ya Gana Da Ma'aikatan Hukumar

Image
Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya kama aiki. A sanarwar da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Yusuf Abubakar Ibrahim ya sanyawa hannu, tace Za a iya tunawa a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labari, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano domin ya kammala wa’adinsa bisa ga umarnin Kotu. Barista Rimin Gado ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru domin dawo da martabar hukumar. Ya bukaci shuwagabanni da ma’aikatan hukumar da su ba shi dukkan goyon bayan da ake bukata domin cimma burin da ake bukata. Ya kuma bukaci Ma’aikatan da su kara himma wajen gudanar da ayyukansu domin zai yi iya kokarinsa wajen tallafa musu. Da yake mayar da jawabi, Daraktan Kula da Ma’aikata, Mahmud Haido ya tabbatar wa Shugaban Hukumar da duk wani hadin kai d...

Labari da dumiduminsa :Gwamna Abba Kabir Ya Mayar Da Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado Kan Mukaminsa

Image
Mai Girma Alh. Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Jihar Kano, ya amince da mayar da Barr. Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa, PCACC, domin kammala wa’adinsa. Za a Iya tuna cewa gwamnatin da ta shude ta dakatar da Barr Muhyi daga mukaminsa bisa wasu dalilai. Sanarwar da babban sakataren Yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace Mayar da shi mukaminsa ya fara aiki ne nan take bisa bin umarnin da Kotu ta bayar tun a baya cewa gwamnatin ta mayar da shi