Likitocin Najeriya Sun Fara Gudanar Da Yajin Aikin Gama-Gari
Likitoci Masu Neman Kwarewa a fadin Najeriya sun fara yajin aikin sai abin da hali ya yi daga safiyar nan ta Laraba. Kungiyar likitocin (NARD) ta sanar da shiga yajin aikin ne jim kadan bayan zaman Majalisar Zartarwarta da ya gudana a Legas a ranar Talata. Shugaban kungiyar, Dokta Orji Emeka Innocent, ya dora laifin shigarsu yajin aikin a kan jan kafar Gwamnatin Tarayya wajen biyan bukatunsu da suka jima da gabatar mata. Dokta Orji ya ce sai da kungiyar ta kara wa’adin da suka ba gwamnati da mako biyu domin ta biya bukatun nasu, amma duk da haka, sai da ta kai ga sun yi yajin aikin gargadi na kwana biyar daga ranar 17 zuwa 21 ga watan Yuli da muke ciki, kuma har yanzu gwamnatin ta ki yin abin da ya kamata. Ya kara da cewa kafin a kai ga haka, sai da aka shafe sama da mako bakwai ba tare da gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyoyin da bangarorin suka kulla a zaman sulhun da ministan kwadago ya jagoranta ba, duk kuwa da cewa an sanya wa’adin aiwatar da su Bukatun likitocin s...