Posts

Showing posts with the label Ceto

An ceto mutane 386 bayan shekaru 10 a hannun Boko Haram

Image
Sojoji sun ceto fararen hula 386, akasarinsu mata da kakanan yara, daga Dajin Sambisa, bayan Boko Haram ta sace su kimanin shekaru goma da suka gabata. Mai rikon mukamin Babban Kwamandan Birget Din Sojin Kasa Na 7, Birgedia AGL Haruna, ne ya bayyana haka ranar Lahadin yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dajin da ke karamar hukumar Konduga ta jihar Borno sakamakon nasarar kammala wani aiki na kwanaki 10 da aka yi wa lakabi da “Operation Desert Sanity 111”. A cewarsa, an kai farmakin ne da nufin kawar da duk wani burbushin Boko Haram da sauran ’yan ta’adda da ke dajin gami da bayar da dama ga masu son mika wuya su yi hakan. Janar Haruna ya bayyana fatansa na cewa karin ’yan ta’adda za su mika wuya, inda ya bayyana yadda suke ci gaba da mika wuya ga sojoji. “Kokarin da muke yi shi ne mu tabbatar da cewa mun kawar da ragowar ’yan ta’adda a Sambisa, tare da bai wa masu son mika kansu damar yin hakan. “Da wannan aiki, muna sa ran da yawa daga cikinsu za su mika wuya

Gwamnan Katsina Ya Ceto Wanda Yan Ta'adda Suka Sace

Image
Gwamnan Katsina, Dikko Raddah, ya jagoranci fatattar ’yan bidiga a kauyen Zakka a Karamar Hukumar Safana ta jihar. Gwamnan ya jagornaci jami’an tsaro hadin gwiwa wajen ceto wani matashi da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi. Dikko Radda ya jagoranci kai daukin ne a lokacin da ya je karamar hukumar kaddamar da shirin tallafi na mataimakin shugaban majalisar jihar, Abduljalal Runka. Sakataren yada labaran gwamna, Kaula Mohammed, ya ce kafin kaddamar da tallafin ne jami’an tsaro suka samu kiran gagawa cewa ’yan ta’adda sun kai hari kauyen Zakka. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Kaula na cewa, nan take gwamnan ya dakatar da shirin, shige gaba aka fattaki ’yan bindigar, aka ceto matashin. Daga nan gwamnan ya ba da umarnin kai mutumin asibiti domin kula da shi, saboda harbin sa da aka yi a kafa.

'Yan sandan Najeriya sun ceto mutane 58 daga hannun 'yan bindiga

Image
  ‘Yan sanda a Najeriya sun ce sun ceto mutane 58 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jihar Kogi, yayin da daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da sun ya rasa ransa yayin artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan ta’addan A cikin wata sanarwa da kakakin rundinar ‘yan sandan jihar Josephine Adeh ta fitar a wannan Lahadin, ta ce wannan nasara da suka samu wani bangare ne na aikin hadin gwiwa tsakanin rundunar da sauran jami’an tsaro, tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarautan jihar.  Adeh ta ce lamarin ya faru ne a dajin Udulu da ke Karamar Hukumar Gegu mai nisan kilomita 145 daga bababban birnin tarayya kasar.  A cewarta, an yi musayar wuta tsakanin ‘yan ta’addan da kuma jami’an tsaro kuma daga bisani suka tsere suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.   Sai dai bata bayyana inda aka sace mutanen ba da kuma tsawon lokacin da suka dauka a hannun ‘yan ta’addan.   RFI