Posts

Showing posts with the label Sulhu

Abin Da Ya Kawo Cikas A Sulhun ECOWAS Da Sojin Nijar — Yusuf Tuggar

Image
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce sun yi tayin tattaunawa domin kawo ƙarshen tankiyar da ke tsakanin Ƙungiyar Raya Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da sojojin da suka kifar da Shugaban Nijar Mohammed Bazoum, amma hakan bai yiwu ba, don kuwa shugabannin sojojin sun ƙi amincewa da yunƙurin. Ambasada Tuggar ya faɗi hakan ne a wata hirarsa da BBC, yana mai cewa duk wata magana da ta shafi a saki Shugaba Bazoum, sojin ba su amince da ita ba. ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 2 a Imo Abdul Amart ya siya wa iyalan Aminu S. Bono gida “Sun ce kar ma a yi wannan maganar, kar ma a sa shi cikin sharuɗɗan yin sulhu,” in ji Yusuf Tuggar. Ya bayyana cewa babu ta yadda za a iya samun sulhu a wannan yanayi. “Za su ci gaba da rike shi kenan ya yi zaman dindindin a kulle?” Ministan ya ce sojojin da suka yi juyin mulki ne suka janyo wa Nijar takunkumin da ECOWAS ta ƙaƙaba mata, da kuma shiga halin da take ciki. Ya ce abin da suke buƙata shi ne a saki Shugaba Bazou

Muna Kan Tataunawa Da Kwankwaso Da Obi - Atiku

Image
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) Rabi’u Musa Kwankwaso domin samun goyon baya da hadin gwiwa. A wata hira da BBC Hausa, Atiku ya ce yana kuma tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi. Ya ce ‘yan biyun Obi da Kwankwaso ba su da wata barazana ga damarsa a zaben. “Ban ga wata barazana domin ba ma tare da su (Kwankwaso da Obi). Muna cikin tattaunawa da su, watakila daya daga cikinsu ya zo,” inji shi. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) Rabi’u Musa Kwankwaso domin samun goyon baya da hadin gwiwa. A wata hira da BBC Hausa, Atiku ya ce yana kuma tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi. Ya ce ‘yan biyun Obi da Kwankwaso ba su da wata ba