Ana ɓarnata kuɗin gwamnati a Majalisar Dokokin Tarayya - Shekarau
A Najeriya, tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ɗan majalisar dattijan ƙasar, Ibrahim Shekarau ya ce kasar ba ta bukatar majalisar dattawa da ta wakilai, kasancewar aiki iri ɗaya suke yi. A nasa ra'ayin, ɓata kudi ne kawai gwamnati ke yi wajen tafiyar da majalisun biyu. Najeriya na da zauruka biyu na majalisar dokokin tarayya, wadda ta haɗa da Majalisar Dattaijai mai wakilai 109. Sai kuma Majalisar Wakilan Tarayya, wadda take da wakilai 360. A tattaunawarsa da BBC, Shekarau ya ce kamata ya yi Najeriya ta rungumi tsarin mulki irin na Birtaniya, wanda aikin ƴan majalisar bai wuce na wucin-gadi ba. Sai dai Shekarau ya ce gyara irin tsarin na majalisar dokoki a Najeriya abu ne mai matuƙar wahala domin sai an yi gyara a kundin tsarin mulkin ƙasar. Kuma cewarsa, akwai yiwuwar ƴan majalisar dokokin, waɗanda dole ne sai an samu amincewarsu kafin a iya sauya dokar, ba za su goyi bayan canza ta ba. Sanata Shekarau ya ce “kowane daga cikin ƴan majalisar tarayya 469, an ba shi dama ya ɗauk...