Posts

Showing posts with the label SIYASAR NAJERIYA

Abin da Shekarau ya ce kan dakatar da Betta Edu

Image
  Jagororin adawa a Najeriya na ci gaba da mayar da martani kan matakin shugaban kasar na dakatar da ministar ma'aikatar jin-kai da ake zargi da rashawa. Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibahim Shekarau na cikin wadanda suka yaba wa shugaba Bola Tinubu duk da cewa wasu 'yan hamayyar na ganin matakin dakatar da ministar ya makara, ya kamata tun kafin naÉ—ata mukamin a tantance halinta. Sai dai Malam Shekarau ya ce sun jinjinawa shugaba Tinubu, da yi wa gwamnatinsa fatan alkhairi. Saboda a ra'ayinsu duk wanda ya yi daidai ya kamata a yaba ma sa da karfafa masa gwiwa da bashi shawarar ci gaba da aikata hakan. ''Mun ga abubuwan da suka faru a baya, misali lokacin da ake zargin sakataren gwamnatin tarayya da aikata ba daidai ba, da cuwa-cuwar kudi da ayyuka, sai da aka yi watanni shida ba tare da an dakatar da shi ba, kuma har yanzu ba mu sake jin duriyar maganar ba. Dan haka wannan mataki da Tinubu ya dauka a bisa adalci abin da ya kamata ya yi kenan,'' in ji She...

Ana É“arnata kuÉ—in gwamnati a Majalisar Dokokin Tarayya - Shekarau

Image
  A Najeriya, tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon É—an majalisar dattijan Æ™asar, Ibrahim Shekarau ya ce kasar ba ta bukatar majalisar dattawa da ta wakilai, kasancewar aiki iri É—aya suke yi. A nasa ra'ayin, É“ata kudi ne kawai gwamnati ke yi wajen tafiyar da majalisun biyu. Najeriya na da zauruka biyu na majalisar dokokin tarayya, wadda ta haÉ—a da Majalisar Dattaijai mai wakilai 109. Sai kuma Majalisar Wakilan Tarayya, wadda take da wakilai 360. A tattaunawarsa da BBC, Shekarau ya ce kamata ya yi Najeriya ta rungumi tsarin mulki irin na Birtaniya, wanda aikin Æ´an majalisar bai wuce na wucin-gadi ba. Sai dai Shekarau ya ce gyara irin tsarin na majalisar dokoki a Najeriya abu ne mai matuÆ™ar wahala domin sai an yi gyara a kundin tsarin mulkin Æ™asar. Kuma cewarsa, akwai yiwuwar Æ´an majalisar dokokin, waÉ—anda dole ne sai an samu amincewarsu kafin a iya sauya dokar, ba za su goyi bayan canza ta ba. Sanata Shekarau ya ce “kowane daga cikin Æ´an majalisar tarayya 469, an ba shi dama ya É—auk...

Ganawar da ‘yan majalisar wakilan jam’iyyun adawa suka yi a Najeriya sun yi azarÉ“aÉ“i - Masana

Image
  Masu sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya na ci gaba da tsokaci a kan ganawar da ‘yan majalisar wakilan da suka fito daga bangaren jam’iyyun hamayya suka yi a makon nan. Ganawar dai ta samu halartar sabbin ‘yan majalisun da kuma wadanda aka sake zaba domin wakiltar jama’arsu a majalisa ta 10 da ake shirin kafawa a watan Yunin 2023. Farfesa Kamilu Sani Fagge, malami ne a tsangayar siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano, ya shaida wa BBC cewa, irin wannan ganawa rikita-rikitar siya ce kawai. Ya ce: “ A gaskiya sun yi sauri wajen gudanar da wannan taro, to amma ina ga sun yi kokari ne da ake cewa a tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro domin idan an zo an rantsar da majalisar, kuma ba su yi wani abu da zai kawo rudani ba, to ko shakka babu ba za a yi da su a majalisar ba.” Ya ce, ya kamata ‘yan majalisar da suka yi wannan taro su sani cewa har yanzu fa akwai sauran zaben ‘yan majalisun da ba a kammala su ba. Malamin ya ce: “ A ka’idar zabe na majalisar wakilai kafin a ce jam’iyya na da rinjay...

Yadda masu son muƙamin shugaban majalisa ke sayen ƙuri'un sanatoci - Ndume

Image
  A Najeriya bayan kammala zaÉ“ukan Æ™asar a yanzu hankali ya karkata kan shugabancin zaurukan majalisun dokoki. Tuni dai wasu 'yan majalisun da ke son É—arewa kujerun shugabancin majalisun suka fara bayyana sha'awarsu ta hanyar kamun Æ™afa a wajen masu ruwa da tsaki na jam'iyyunsu da kuma zaÉ“aÉ“É“un 'yan majalisar. Sai a watan Yuni mai zuwa ne za a Æ™addamar da majalisar dokokin ta goma, daga nan kuma a fara shirye-shiryen zaÉ“en shugabannin majalisun. To sai dai wasu 'yan majalisun sun fara zargin cewa ana amfani da kuÉ—i wajen sayen bakin 'yan majalisun domin zaÉ“en wasu a matsayin shugabannin majalisun. Sanata Ali Ndume É—an majalisar dattawa ne daga jihar Borno ya kuma shaida wa BBC cewa akwai zargin da ake yi na cewa wasu na amfani da kuÉ—i wajen ganin sun samu É—arewar kujerar shugaban majalisar dattawa. Ya ce a yanzu siyasar Æ™asar masu hannu da shuni, ko masu kuÉ—i su ne ke juya É“angaren siyasar Æ™asar. ''Dandalin siyasarmu ya cika da irin waÉ—annan mutanen da s...

Babu abun da zai hana a gudanar da zabe a Najeriya - Gwamnati

Image
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa da al’ummar kasar cewa babu abin da zai hana gudanar da babban zaben kasar da ke tafe a watannin Fabariru da Maris din shekarar da muke ciki ta 2023 duk da barazanar tsaron da kasar ke fuskanta. Minstan yada labarai na Najeriyar, Lai Mohammed wanda ya bayyana haka a Abuja, ya ce gwamnati ba ta sauka daga kudirinta na gudanar da zabe kamar yadda aka tsara ba. Kalaman gwamnatin dai na zuwa ne bayan hukumar zaben kasar mai zaman kanta INEC ta yi kashedi cewa idan har ba a shawo kan matsalar tsaron da wasu sassan kasar ke fama da shi ba, babban zaben kasar na iya faskara. A cewar INEC ko da an iya gudanar da zaben a wasu sassan alamu na nuna cewa babu tabbacin iya gudanar da su a wasu sassa saboda matsalar ta tsaro, lamarin da tuni ya haddasa cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya. Haka zalika tuni, masana tsaro suka fara nuna yatsa ga hukumar ta INEC wadda suka ce bata da hurumin sanar da wannan mataki a radin kanta har sai ta tuntubi bangarorin...