Wa'adin Dena Karbar Tsofaffin Kudi Ya Cika - CBN
Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya jadadda cewar ranar 10 ga watan Fabrairu ne wa’adin amfani tsofaffin takardun Naira ya cika. Emefiele ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da jami’an diflomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Waje da ke Abuja a ranar Talata. “Lamarin ya lafa sosai tun bayan lokacin da aka fara biyan kudi a kan kanta wanda hakan ya rage dogayen layuka a ATM. “Don haka babu bukatar la’akari da wani sauyi daga wa’adin ranar 10 ga Fabrairu,” in ji shi. Bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rudani game da umarnin kotun kolin wanda ta tsawaita wa’adin zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu, don yanke hukunci kan karar da ke gabanta. ‘Yan Najeriya sun shiga rudani yayin da bankunan kasuwanci suka daina karbar tsoffin takardun tun daga ranar Litinin. Da yake karin haske, Emefiele ya ce, “Wasu daga cikin shugabanninmu suna siyan sabbin takardun kudi suna ajiyewa saboda wata manufa saboda haka ba zan iya yin karin haske kan hakan ba.” Em...