Hajj2024: NAHCON Ta Tura Tawagar Farko Zuwa Saudia
A gobe ne Tawagar Jami'an Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) su 43 za su tashi daga Abuja zuwa kasar Saudia domin fara gudanar da aikin Hajin bana A sanarwar da mataimakin daraktan yada yada da dab'i na hukumar, Mousa Ubandawaki, yace Tawagar da ta kunshi Jami’an Hukumar NAHCON 35 da Ma’aikatan Lafiya 8 za su je kasar Saudiyya domin shirin karshe na karbar Alhazan Najeriya daga Jihar Kebbi da za su isa Masarautar a ranar Laraba 15 ga watan Mayu domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024. Da yake jawabi ga tawagar a wani dan takaitaccen biki na bankwana da aka gudanar a dakin taro na hukumar, Shugaban Hukumar Malam Jalal Ahmad Arabi ya taya tawagar murna da zaben da aka yi musu, sannan ya bukace su da su yi rayuwa mai kyau ta hanyar gudanar da ayyukansu kamar yadda aka umarce su. Don haka dole ne ku tashi tsaye domin samun ladan mu anan da na Allah a Lahira na kyautatawa baqonsa. Su ne dalilin da ya sa kuke wurin, don haka a kowane lokaci ku tabbatar da