Gwamnan Kano Ya Kaddamar Da Rabon Tallafin Kudi Ga 'Yan Mata' Yan Makaranta 45 850 Karkashin Shirin AGILE
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin raba katin ATM na kudi da ya kai naira miliyan 917 ga ‘yan mata 45850 karkashin shirin samar da ‘yan mata na matasa (AGILE) wanda aka gudanar a makarantar sakandiren mata ta gwamnati ta Janguza. a karamar hukumar Tofa. A sanarwar da mai rikon mikamin babban sakataren yada labaran Gwamnan, Hisham Habib ya sanyawa hannu, a cewar Gwamnan, an zabo wadanda suka ci gajiyar tallafin ne daga kananan hukumomi 19 na jihar wadanda ba su da ilimi sosai kuma aikin ya hada da samar da alawus-alawus, gyarawa da gina ajujuwa domin koyarwa da koyo. Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta fannin ilimi yana mai cewa, “kamar yadda muka yi alkawari a lokacin yakin neman zabe, za mu tabbatar da aiwatar da ilimi kyauta tare da samar da abubuwan da ake bukata domin tabbatar da gudanar da ayyukansa ta yadda yara masu zuwa makaranta a yi ilimi” Gwamnan ya nanata. Dangane da karbar kudaden haram da masu kula da makarantu ke...