Posts

Showing posts with the label Afuwa

Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni Sama Da Dubu Hudu Afuwa A Cikin Shekaru Takwas

Image
  Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi afuwa ga fursunoni dubu hudu da goma sha uku a cikin shekaru takwas a fadin gidajen gyaran hali na Kano.  Haka kuma a cikin shekaru takwas gwamnatinmu ta biyan tara da diyya ga fursunonin da suka kai naira miliyan hudu da dubu dari tara da arba’in da tara.  Gwamnan wanda ya sami wakilcin mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana haka a lokacin da ya yi afuwa ga fursunoni 43 da suka aikata laifuka daban-daban kuma suke zaune a gidan yari, a yayin bikin karamar Sallah da aka yi a gidan yari na Goron Dutse. Ganduje ya jaddada cewa ’yanci shi ne komai na rayuwar dan Adam, ya yi kira ga fursunonin da aka yi wa afuwar da su nuna kyawawan halaye a duk inda suka samu kansu a cikin al’umma. A jawabinsa Kwanturola na hukumar gyaran jiki a jihar kano, Suleiman Muhammad Inuwa ya bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na yin afuwa ga fursunonin da biyan tara, diyya ya tai...