Posts

Showing posts with the label Jami'an tsaro

Jami'an Tsaro Sun Rufe Ofishin PDP Na Jahar Ondo

Image
Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS da kuma ’yan sanda sun rufe sakatariyar jam’iyyar adawa ta PDP ta Jihar Ondo. Hukumomin tsaron sun dauki matakin ne a safiyar Litinin a daidai lokacin da al’ummar jihar suke gunaguni da neman gwamnatin jihar ta bayyana musu inda Gwamna Rotimi Akeredolu yake da kuma halin da yake ciki. Yadda Ba Da Dala Ga Masu Shigo Da Shinkafa Zai Shafi Farashin Ta Gida Ganduje ya lashi takobin kare kujerar gwamnan Nasarawa da kotu ta kwace Ana zargin hukumomin tsaron sun rufe ofisihin jam’iyyar ne sakamakon shirin wasu ’yan jam’iyyar na gudanar da zanga-zanga kan rashin kasancewar gwamnan a jihar na tsawon lokaci. Da farko Gwamna Akerodule wande ke fama da rashin lafiya da ba a bayyana ba, ya shafe wata uku a kasar Jamus, inda yake jinya, kafin ya dawo jihar a watan Satumba. Tun bayan dawowar gwamnan, ya ci gaba da zama a gidansa, da ke birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, lamarin da ya sa babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar kiraye-kirayen ya sauka daga mu...

Yadda jami'an tsaro suka tsare Peter Obi a London

Image
  Kwamitin yaÆ™in neman zaÉ“en shugaban Æ™asa na jam’iyyar LP ya ce jami’ai sun tsare tare da hantarar É—an takarar shugaban Æ™asa na jam’iyyar, Peter Obi a birnin London. Mai magana da yawun kwamitin kamfe na jam’iyyar LP, Diran Onifade ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba. Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a filin jirgin sama na Heathrow da ke London. Ta Æ™ara da cewa jami’an shige da fice na Birtaniya É—in ne suka titsiye tsohon É—an takarar shugaban Æ™asar. Diran Onafide ya ce hukumomi a Birtaniya sun tsare tare da yin tambayoyi ga tsohon gwamnan na jihar Anambra kan wani lamari da ya shafi wani mutum da ke yin sojan-gona da suna Peter Obi. Sanarwar ta Æ™ara da cewa jami’an sun sassauta wa Petetr Obi ne bayan wasu Æ´an Najeriya da ke a filin jirgin sun sanya baki. Peter Obi dai ya isa birnin na London ne domin bukukuwan Easter na mabiya addinin Kirista. Bayanin ya nuna cewa bayan saukar Peter Obi a filin jirgin na Heathrow da ke London, jami’an tsaro sun zo ...

Kofa Ya Gudanar Da Taron Addu'a, Godiya Da Kuma Sako Ga Jami'an Tsaro Da Hukumar Zabe

Image
A ranar Asabar ce sabon zababben dan majalissar tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa PhD, ya jagoranci Sallar Nafila tare da addu'oi da godiya ga Allah da al'umma bisa nasara da Allah ya bashi a zaben da ya gabata  Haka kuma an gudanar da addu'oi na musamman wa mai girma Madugu Sen Rabiu Musa Kwankwaso da addu'oin samun nasarar Engr Abba Kabir Yusif da yan takararsu na majalisar jiha a Bebeji da Kiru da kano a zabe mai zuwa. A hanu guda kuma Kofa ya kaddamar da tsare tsare na musamman akan zabe mai zuwa kuma yayi kira da babbar murya ga jami'an tsaro da ma'aikatan zabe wanda aka turo su Kano, akan su tabbatar sun tsaya akan gaskiya don samun zaman lafiya a kano

Jami'an tsaro sun kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasan Edo 12

Image
Hukumomin jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya ta ce an kuɓutar da fasinjoji 12 na jirgin ƙasa, da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a tashar jiragen ƙasa da ke jihar a makon da ya gabata. An kama wasu daga cikin 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su, to sai dai wasu daga cikinsu sun tsere tare da wasu fasinjojin biyu a lokacin da jami'an tsaro ke ƙoƙarin kuɓutar da su. Hukumomin jihar sun ce an kuɓutar da mutanen 12 a lokacin da jami'an tsaro suka yi wa masu garkuwa da mutanen kwanton ɓauta. Tuni aka kai mutanen da aka kuɓutar ɗin asibiti domin duba lafiyarsu. Gwamnatin jihar ta alƙawarta ci gaba da nemo sauran fasinjojin biyu da ke hannun 'yan bindigar. Gwamnan jihar ya soki hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta ƙasar kan gaza samar da tsaro kan tasoshin jiragen ƙasan duk da faruwar makamancin wannan hari a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar a shekarar da ta gabata. Tun da farko dai hukumomin sun ce mutum 32 ne 'yan bindigar suka yi garku...