Muna Asarar N13bn Duk Mako Saboda Rufe Iyakar Najeriya Da Nijar – ’Yan Kasuwa
’Yan kasuwar Arewacin Najeriya sun koka da cewa suna tafka asarar sama da Naira biliyan 13 duk mako saboda rufe iyakokin Najeriya da Nijar sanadiyyar rikicin kasar. A ranar 4 ga watan Agusta, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ba hukumar Kwastam umarnin rufe dukkan iyakokin kasar da Jamhuriyar Nijar. Iyakokin sun hada da ta Jibiya da ke Jihar Katsina da ta Illelah a Jihar Sakkwato da kuma ta Maigatari a Jihar Jigawa. Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi, Shugaban kungiyar ’yan kasuwa na Arewacin Najeriya, Ibrahim Yahaya Dandakata, ya ce matakan da aka dauka sun jefa su cikin tsaka mai wuya. Sai dai ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta taimaka ta bude iyakar Maje-Illo da ke Jihar Kebbi, domin ta ba su damar shigo da kayayyaki cikin kasa. A cewarsa, “Tun bayan umarni Shugaban Kasa kan rufe dukkan iyakokin Najeriya da Nijar sakamakon juyin mulkin da aka yi a can, muke cikin tsaka mai wuya. ’Yan kasuwar Arewa na tafka asar Naira biliyan 13 kowanne mako. “Galib...