Posts

Showing posts with the label Atiku

Atiku Abubakar Zai Kaddamar Da Makarantar Haddar Alkur'ani A Kano

Image
  Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai kaddamar da makarantar sakandaren kwana ta haddar Al-Kur’ani mai dalibai 500 a Jihar Kano. Atiku zai bude wannan makarantar haddar Al-Kur’ani ce a unguwar Gunduwawa da ke Karamar Hukumar Gezawa, a yayin ziyarar yakin neman zabensa a Jihar Kano, wadda za a gudanar ranar 9 ga watan Fabrairun da muke ciki. Wannan makarantar haddar Al-Kur’ani “Na da wurin kwanan dalibai mata 250, maza 250, kuma za su rika haddace Al-Kur’ani a cikin wata bakwai, kafin su tafi makarnatun gaba da sakandare,” inji kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku a Jihar Kano, Sule Ya’u Sule. Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ne dai ya gina makarantar ta haddar Al-Kur’ani mai daukar dalibai 500 a matsayin aikinsa na raya alu’m Sule Ya’u Sule ya sanara ranar Laraba cewa, Atiku zai kaddamar da makarantar ce a ranar taron yakin neman zabensa, ko kuma washegari. A cewarsa, “Wazirin Adamawa zai zo Kano ranar 9 ga Fabrairu, don haka j

Muna Kan Tataunawa Da Kwankwaso Da Obi - Atiku

Image
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) Rabi’u Musa Kwankwaso domin samun goyon baya da hadin gwiwa. A wata hira da BBC Hausa, Atiku ya ce yana kuma tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi. Ya ce ‘yan biyun Obi da Kwankwaso ba su da wata barazana ga damarsa a zaben. “Ban ga wata barazana domin ba ma tare da su (Kwankwaso da Obi). Muna cikin tattaunawa da su, watakila daya daga cikinsu ya zo,” inji shi. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) Rabi’u Musa Kwankwaso domin samun goyon baya da hadin gwiwa. A wata hira da BBC Hausa, Atiku ya ce yana kuma tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi. Ya ce ‘yan biyun Obi da Kwankwaso ba su da wata ba

Bayan Ficewa Daga Tafiyar Tinubu, Naja’atu Ta Koma Wajen Atiku

Image
  Fitacciyar ’yar siyasar nan ta Jihar Kano kuma daya daga cikin tsofaffin Daraktocin kamfen din dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, Naja’atu Muhammad, ta koma wajen dan takarar PDP, Atiku Abubakar. Matakin nata na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan ta sanar da ajiye mukamin na Tinubu, tare da ayyana ficewarta daga jam’iyyar mai mulki. Ta tabbatar da hakan ne yayin ziyarar da ta kai wa Atiku a gidansa ranar Lahadi. Daga bisani dai ta shaida wa  Aminiya  cewa yanzu tana goyon bayan takarar ta Atiku a zabe mai zuwa. A baya dai, Naja’atu, wacce ita ce Daraktar Kungiyoyin Fararen Hula a Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu, ta ce za ta gana da ’yan takarar jam’iyyun siyasa kafin ta dauki matsaya kan wanda za ta mara wa baya. Ta ce ta dawo daga rakiyar Tinubu ne saboda a cewarta, sam ba ya iya yin tunani da kansa. Ta ce, “Gaskiya ne yanzu ba na yin Tinubu, dalili ke nan ma da na bar jam’iyyar. Abubuwa da dama sun faru, da kyar yake iya tunani da kwakwalwarsa. Wannan ko shakka babu,

Zan Kammala Aikin Tashar Jiragen Ruwa Ta Baro Idan Kuka Zabe Ni – Atiku

Image
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin kammala aikin tashar jiragen ruwa ta Baro da ke Jihar Neja, muddin aka zabe shi a zabe mai zuwa. Atiku ya kuma ce jam’iyyarsa ce kawai take da siddabarun da za ta magance kalubalen tsaro da ya addabi kasar, musamman ma Jihar Neja. Burkina Faso ta ba sojojin Faransa wata daya su fice daga kasarta Ya yi wadannan alkawuran ne lokacin da yake jawabi ga wasu kusoshi da magoya bayan jam’iyyar a Minna, babban birnin Jihar Neja ranar Asabar. Atiku ya ce PDP ce ta faro aikin na Baro rimi-rimi lokacin da take mulki, amma APC na zuwa ta yi watsi da shi. A cewar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, “Muna addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya a Jihar nan. Kun san PDP ce kawai za ta iya dawo da zaman lafiya a Neja. Lokacin da take mulki daga 1999 zuwa 2015, akwai matsalar tsaro a Neja? Muna so mu tabbatar muku cewa muddin PDP ta dawo, matsalar za ta zama tarihi. “Muna kuma so mu tabbatar muku cewa aikin tashar Ba

Duk Mai Son Mukami A Gwamnanatina Sai Ya Kawo Akwatinsa Lokacin Zabe - Atiku

Image
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce duk dan jam’iyyar da ke neman kwagila ko mukami a gwamnatinsa, sai ya nuna sakamakon zaben mazabarsa kafin a ba shi. Atiku ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abekuta babban birnin Jihar Ogun, yayin taron ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar. Atiku ya ce halartar kowanne yakin neman zaben jam’iyyar ba shi ne tabbacin samun matsayi ko kwangila a gwamnatinsa ba, jajircewa wajen ganin an kawo akwatinan mazaba ne. Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya kuma ce, “Dukkanku magoya bayan PDP ne, kuma kuna so ta dawo mulki, don haka ina rokonku ku tabbatar kun kawo akwatinan mazabunku. Yawon zuwa yakin neman zaben kafatanin ’yan takarar jam’iyya ba shi ne zai sa ka samu aiki ko matsayi ko kwangila ba idan an ci zabe, hanyar da kadai za ku samu shi ne nuna min sakamakon zaben mazabarku. “Kuma ina bai wa kowanne dan takarar PDP umarnin yin hakan, domin da haka ne kadai za mu ci zabe. Atiku ya kuma yi alkawarin farfado