Zamu duba yiwuwar taimakawa Burundi da man Fetur - Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ƙasar za ta duba buƙatar taimakon makamashi, musamman man fetur da gwamnatin ƙasar Burundi ta gabatar wa ƙasarsa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adeshina ya sanya wa hannu, shugaba Buhari ya yi alƙawarin ne bayan karɓar baƙuncin ministan kuɗi , kasafi da tsare-tsare na ƙasar Burundi Audace Niyonzima a fadarsa da ke Abuja.
Sanarwar ta ce Buhari ya tabbatar wa da mista Niyonzima cewa Najeriya za ta taimaka wa ƙasar Burundi ta hanyoyi da dama ƙarƙashin inuwar zumunci da 'yan uwantaka da ke tsakanin ƙasashen Afirka.
Shugaba Buhari ya ƙara da cewa ya san yadda ƙasa ke ji musamman idan tana fama da ƙarancin makamashi, tare da alƙawarta cewa zai tura batun ga babban kamfanin mai na ƙasar NNPC domin duba buƙatar.
Buhari ya ce a yanzu batun zaɓen ƙasar, da batun saukarsa daga mulki ne a gabansa, tun da dai ya yi wa'adi biyu da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi dama.
A nasa ɓangare ministan na Burundi ya yi wa ƙasar fatan alkairi a manyan zaɓukan da za ta gudanar cikin wannan shekara.