Posts

Showing posts with the label Zargin cin hanci

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Kano Ta Shigar Da Karar Tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, Matarsa, Hafsat Wasu Mutane 6 A Kotu Akan Zargin Cin Hanci Da Rashawa

Image
Gwamnatin jihar Kano ta shigar da karar tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat Umar, Umar Abdullahi Umar da wasu mutane biyar a gaban kotu bisa zarge-zarge 8 da suka hada da cin hanci da rashawa da karkatar da wasu kudade da suka shafi biliyoyin naira. Wannan yana kunshe ne a cikin takardar tuhuma mai kwanan wata 3 ga Afrilu, 2024 tare da jerin shaidu 15 da aka makala. SOLACEBASE ta ruwaito cewa sauran wadanda ake kara a karar sun hada da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises. , Cikakken labarin zai zo muku nan gaba kadan 

Zargin Cin Hanci: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Dakatar Da Manajan Darakta Na Kamfanin KASCO

Image
A ci gaba da kokarinsa na yaki da cin hanci da rashawa, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayar da umarnin dakatar da Manajan Daraktan Kamfanin Samar da Aikin Gona na Kano (KASCO) Dakta Tukur Dayyabu Minjibir. A sanarwar da babban sakataren yada yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, Gwamnan ya bayar da umarnin dakatarwar ne a wata mai kwanan wata 12 ga Satumba, 2023 wanda sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya mika. An dakatar da Manajan Darakta bisa zargin hannu a sayar da hatsin da bai dace ba na Gwamnatin Jihar Kano. Ya Bada Umurnin Binciken Gaggawa yayin da Gwamna Ya Nanata Alkawarin Rashin Hakuri Kan Cin Hanci da Rashawa An Kuma umurci Dakta Dayyabu da ya mika al’amuran kamfanin ga babban jami’i a Hukumar nan take har sai an kammala bincike.

Birtaniya Ta Gurfanar Da Diezani A Gaban Kotu Kan Zargin Almundahana

Image
Kasar Birtaniya ta gurfanar da tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke a gaban kotu kan zargin rashawa lokacin da take Minista. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa ’yan sandar kasar sun ce sun maka ta a kotun ne saboda suna zargin ta karbi cin hanci a wasu kwangilolin man fetur da iskar gas. Diezani, mai shekara 63 a duniya, na daya daga cikin kusoshi a gwamnatin tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan. A zamanin mulkin tsohon Shugaban, Diezani ta rike mukamin Ministar Mai ta Najeriya daga 2010 zuwa 2015, sannan ta rike matsayin shugabar Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta Duniya (OPEC). A cewar Shugaban Hukumar Yaki da Laifuffuka ta Birtaniya (NCA), Andy Kelly, “gurfanarwar da aka yi wa Diezani wata somin-tabi ce na wani zuzzurfan bincike na kasa da kasa da aka dade ana yi.” Hukumar dai ta ce ana zargin Diezani da karbar akalla tsabar kudi har Fam din Ingila 100,000 da wasu motoci da hawa jirgin da ba na ’yan kasuwa ba,