Posts

Showing posts with the label Sarkin Musulmi

Wa’adin Tsofaffin Kudi: Mun Zuba Ido Mu Ga Yadda CBN Zai Kare Da Mutanen Karkara —Sarkin Musulmi

Image
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce Babban Bankin Najeriya (CBN) bai sanya su cikin masu ruwa da tsaki ba kan batun sauya fasalin takardun kudi, dalilin ke nan da suka zuba ido su ga yadda zai kare da mutanen karkara idan wa’adin karbar tsohuwar naira ya cika. Sarkin ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin Babban Jami’in Gudanarwa na CBN shiyyar Sakkwato, Dahiru Usman hadi da wasu jami’an babban bankin ranar Alhamis a fadarsa. Alhaji Bako Zuntu ya riga mu gida gaskiya Duk da gargadin CBN har yanzu bankuna na bai wa mutane tsohuwar naira ta na’urar ATM Abubakar ya ce kamata ya yi a ce CBN din ya sanya dukkanin masu ruwa da tsaki tun a matakin farko na sauya takardun na naira, amma sai ya yi biris da sarakunan gargajiya. “Akwai mutanen karkarar ma da ba su san an sauya kudin ba kwata-kwata, kuma idan ka ba su sabo ba za su karba ba saboda za su zaci na bogi ne. “Mu ne muke kusa da su, mu ne kuma ke da hanyoyin isar musu da sakon, don bibiyar kafafen yada labarai