‘Yan sanda sun fara farautar shugaban INEC na Adamawa
Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya umurci wata tawagar 'yan sanda ta yi aiki tare da hukumar zaben Najeriya INEC wajen bincike da kuma gurfanar da shugaban hukumar zabe na jihar Adamawa da aka dakatar Hudu Yunusa Ari. A wata sanarwar da rundunar ta fitar wacce kakakinta Olumuyiwa Adejobi ya sanya wa hannu, babban sufeton ya ce 'yan sanda za su tabbatar sun yi dukkan mai yiwuwa domin gano dalilin da ya sa Hudu aikata abun da ya yi. Ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen gwamna na jihar Adamawa da aka ƙarasa ne sai kwatsam Hudu wanda shi ne kwamishinan zaɓe na jihar, ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen. IGP Usman ya ce a shirye su ke su tabbatar an yi hukunci da ya dace kan dukkan wadanda aka samu da hannu a lamarin da ya faru a Adamawa domin martaba dokokin dimokradiya. Sanarwar ta tabbatar wa 'yan Najeriya da kuma kasashen duniya cewa 'yan sanda za su binciki ayyana Aishatu Binani ta APC da Hudun ya yi tare saur...