Yanzu-Yanzu: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Nada Shahararren Dan Kannywood A Shugaban Hukumar Tace Finafinai
Gwamnan Jihar Kano Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin shugabannin hukumomin gwamnati. Wadanda aka nada kamar yadda babban sakataren yada labaran gwaman, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanar, sune kamar haka. 1. Injiniya Ado Ibrahim Umar, Manajan Darakta na Kamfanin Raya Wutar Lantarki ta Kano (KHEDCO) 2. Alh. Auwalu Mukhtar Bichi, Manajan Daraktan Kamfanin Zuba Jari 3. Dr. Farouq Kurawa, Manajan Daraktan Hukumar Noma da Raya Karkara ta Jihar Kano (KNARDA). Har zuwa lokacin da aka nada shi, Dakta Kurawa shi ne Babban Sakataren Gwamnati (PPS) na Gwamna. 4. Dr. Tukur Dayyabu Minjibir, Manajan Daraktan Kamfanin bunkasa Aikin Gona na Kano (KASCO). 5. Hussain Sarki Aliyu Madobi, Manajan Darakta na Sustainable Kano Project (SKP) 6. Sadiq Kura Muhammad, Manajan Darakta na gidan Zoo Kano (ZGK) 7. Injiniya Sani Bala, Manajan Daraktan Hukumar samar da wutar Lantarki a Karkara (REB) 8. Shamwilu Gezawa, hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ta jihar Kano (R...