Hajjin 2023: An Kammala jigilar Alhazan Kano, inda Shugaban Hukumar ya yabawa Gwamna Yusuf
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Kano ta kammala aikin hajjin shekarar 2023 tare da dawo da tawaga ta karshe daga kasar Saudiyya ranar Lahadi. Shugaban hukumar Alhaji Yusuf Lawan ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata a filin jirgin saman Malam Aminu Kano lokacin da ya sauka daga filin jirgin sama na Sarki AbdulAziz na Jiddah na kasar Saudiyya. A sanarwar da mai rikon mukamin Jagoran tawagar 'yan jaridu na aikin Hajji na bana, Nasiru Yusuf Ibrahim ya sanyawa hannu, tace, Alhaji Yusuf Lawan ya bayyana cewa da wannan jirgi na karshe hukumar ta dawo da dukkan tawagar Kano da suka halarci aikin hajjin bana. Ya bayyana cewa gaba dayan tawagar sun nuna dattako da kyawawan halaye a duk lokacin da ake gudanar da aikin ibadar Shugaban ya danganta nasarorin da aka samu a aikin Hajjin bana da gagarumin goyon baya da jagoranci da gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ba hukumar. Ya ce tsohuwar hukumar da gwamnatin da ta shude sun gurbata abubuwa da dama