Hukumar Alhazai Jahar Kano Ta Biya Sama Da Naira Biliyan 18 Ga NAHCON Domin Hajin Bana
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana a yau cewa hukumar ta aikawa hukumar alhazai ta kasa sama da Naira biliyan 18 domin shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin shekarar 2024. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa duk da cewa mutane 3,110 ne suka biya kudin aikin hajji, amma da yawa suna jiran bizarsu daga hukumar alhazai ta kasa. Ya kuma bukaci hukumar da ta hanzarta bayar da bizar kafin rufe ranar, inda ya jaddada kudirin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na kammala gyara a sansanin Alhazai kafin a fara jigilar maniyyata. Darakta Janar din ya kara da cewa, ba kamar shekarar da ta gabata ba, a wannan shekarar gwamnati ta samar da dukkan kayayyakin da ake bukata a sansanin Alhazai gabanin gudanar da aikin hajji domin amfanin Maniyyata ...