Posts

Showing posts with the label Shugaban Jam'iyya

’Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Kanar Din Soja A Zamfara

Image
  ’Yan bindiga sun sace Kanar Lawal Rabiu Yandoto (mai ritaya) a kan hanyarsa ta zuwa garinsu, Yandoto da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Wata majiya ta bayyana cewa ’yan bindigar sun sace shi ne tare da ’ya’yansa biyu da kuma wasu. “Maharan sun yi wa Kanar kwanton bauna da misalin karfe 6 na yamamcin ranar Lahadi, suka sace shi tare da ’ya’yansa biyu da kuma wasu mutum biyu,”  in ji majiyar. Majiyar ta ce an ji karar harbe-harbe daura da shiga garin na Yandoto lamarin da ya tilasta mutane guje-guje domin tsira. Ta bayyana cewa an gano maharan sun yi awon gaba da tsohon Kanar din ne bayan da mutane suka samu motarsa babu kowa a ciki. Kakakin ’yan sandan jihar bai daga waya ba ballatana a ji ta bakinsa kan lamarin. (AMINIYA)