Posts

Showing posts with the label Sanata

Sanatan Kano Ya Ba Dalibai 620 Tallafin Karatu A BUK

Image
  Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibrin ya ba wa daliban mazabarsa 628 tallafin karatu a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Aminiya ta gano cewa duk dalibin mazabar da ya rabauta ya samu tallafin N50,000 daga dan majalisar. Da yake bude rabon tallafin, shugaban ma’aikatan Sanata Barau, Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi, ya ce dan majalisar ya yi haka ne domin ba wa daliban mazabarsa damar neman ilimi a manyan makarantu. Kakakin Mataimakin Shugaban Majalisar, Ismail Mudashir, ya ce daliban mazabar Kano ta Arewa da ke sauran manyan makarantu a fadin Najeriya ma za su amfana da tallafin. Don haka ya bukaci daliban da suka amfana da su yi amfani da abin da aka ba su ta hanyar da ta dace sanna su kara jajircewa wajen neman ilimi. Wani dalibin aji hudu a jami’a da ya samu tallafin , Adama Iliyasu Rabiu, ya yaba wa dan dan majalisar tare da rokon Allah Ya saka masa. (AMINIYA)

Kotun Koli Ta Ba Wa Rufai Hanga Na NNPP Kujerar Sanatan Kano Ta Tsakiya

Image
  Kotun Koli ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta cire sunan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, a matsayin wanda ya ci zaben Sanatan Kano ta Tsakiya. Kotun ta umarci INEC ta maye gurbin Shekarau da sunan Rufai Hanga a matsayin halastaccen wanda ya ci zaben kujerar a karkashin Jam’iyyar NNPP. Ta kuma tabbatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta tabbatar da Rufai Hanga a matsayin halastaccen dan takarar NNPP a zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Maris. INEC dai ta bayyana Shekarau a matsayin wanda ya ci zaben duk kuwa da cewa ya sauya sheka daga NNPP zuwa PDP kuma ya sanar da cewa ya janye daga takarar . AMINIYA