Yarima Harry na Burtaniya ya zargi yayansa Yarima Williams da dukansa
Yarima Harry ya yi da'awar cewar yayansa Yarima William ya taɓa dukan sa, in ji jaridar Guardian, wadda ta ce ta ga wani ɓangare na littafin da yarima Harry ɗin ke rubutawa, mai taken 'Spare'.
Jaridar ta ruwaito cewa littafin ya ambato wani lokaci da aka samu sa-in-sa tsakanin ƴan'uwan biyu a kan matar Harry, Meghan.
Jaridar ta ce a cikin littafin Harry ya rubuta cewa "ya ci kwalata, ya tsinka sarƙar da ke wuyana, sannan ya bugani da ƙasa."
Sai dai Majiyarmu ba ta kai ga ganin littafin na 'Spare' ba.
Ba za a buga littafin ba sai ranar Talata ta sama, amma jaridar Guardian ta ce ta ga littafin a wani abu da ta kira " bugun kafin a wallafa".
Kawo yanzu fadar Buckingham ba ta ce komai ba, duk da cewa an tuntuɓe ta kan batun.bayar da rahoto kan lamarin, ba mu kira shi da faɗa ba, saboda Harry bai mayar da martani ba.
A cewar jaridar Guardian "Yarima Harry ya rubuta cewar ɗan uwansa ya nemi da ya rama bugun da ya yi masa, amma ya ƙi, sai dai daga baya Yarima William ya yi "nadama, ya kuma ba shi haƙuri".
Hotuna sun nuna yadda Yarima Harry ke sanya baƙar sarƙa, a taro irin na wasannin Invictus, da lokacin tafiya zuwa wata ƙasa shi da Meghan, kamar yadda suka yi a watan Satumbar 2019.
Har yanzu kamfanin wallafa littatafai na Penguin Random bai kai ga tabbatar da cewar ko wadancan bayanai da suka fita daga littafin, kan batun da Yarima Harry ya yi cewar yana da saɓani da ɗan uwansa, gaskiya ne ko kuwa akasin haka ba.
A wani fim na rayuwar Harry da Meghan na Netflix, Yarima Harry ya bayyana taron da ya halarta da ɗan uwansa, da mahaifinsa da yanzu ya zama sarki.
Yarima Harry ya bayyana taron farkon shekarar 2020, wanda marigayiya sarauniyar Ingila ta hallarta, da "abin kaɗuwa".
Yarima Harry ya ce "abin kaɗuwa ne, da na ji yayana na ihu da ɗaga murya gare ni, da mahaifina, yana faɗar abubuwa da babu gaskiya a cikinsu, kakata na zaune ta yi shiru tana jin abin da ke faruwa,".
Jaridar Guardian ta ce, Prince Harry ya bayar da cikakkun bayanai kan yadda zamansu ya kasance da Sarki Charles, a lokacin yana Yariman Wales, da Yarima William bayan jana'izar kakansa Yarima Phillip, a Afrelun 2021.
A cewar jaridar, Yarima Harry ya rubuta cewar, mahaifinsa ya shiga tsakaninsu shi da Yarima Williams, yana cewar "don Allah yara kar ku sa shekaruna na ƙarshe su kasance cikin ƙunci".
A wata hira da za a haska a ranar 8 ga watan Janairu, kafin sakin littafin, yariman ya ce: "Zan so na daidaita dangantakata da mahaifina da ɗan'uwana".
Ko da yake Yarima Harry ya shaida wa Tom Bradby na tashar ITV cewar, ba su nuna sha'awarsu ta son a daidaita ba," duk da cewar ba a fahimci taƙamaimai wa yake nufi ba.
Ko da aka tuntuɓi fadar Buckingham kan lamarin, ta ƙi cewa komai a kai.
A wani jawabi da kamfanin wallafa litattafai na Penguin Random ya yi a watan Octoban bara, ya ce "daga ƙarshe - wannan shi ne labarin Harry".
"Da irin tsagwaron gaskiyar da ke cikin littafin Spare, littafi ne da ke cike da bayanai, da tone-tone, da fadin ra'ayin kai, da darusan da ya koya kan mulki da soyyaya kan baƙin ciki.