Har Yanzu Ban Taba Ganin Sabbin Takardun Naira Ba- Gwamna Ortom

Gwamna Jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya bayyana cewa duk da matsayinsa na mai rike da mafar iko amma har yanzu bai taba hada ido da sabbin takardun Naira ba.

Mista Ortom ya bayyana hakan a wannan Larabar yayin da yake kira ga mahukunta da su tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudin kasar.

Gwamnan ya bayyana damuwa dangane da karancin wa’adin amfani da tsohuwar naira da aka bai wa ’yan Najeriya, yana mai jan hankali da a yi la’akari da mazauna karkara da ba su da masaniyar abin da ke faruwa dangane da sauya wa takardun kudin fasali.

Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamnan ya yi wannan koke ne a jawabinsa yayin ziyarar da Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Sarwaaun Tarka ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke birnin Makurdi.

A cewarsa, ­“a matsayina na Gwamna, har yanzu ban yi ido biyu da sabbin takardun Naira ba duk da cewa kwanaki shida kacal suka rage wa’adin amfani da tsohuwar naira ya cika.

“Yanzu a irin wannan yanayi ya za a karke ke nan da mazauna karkara?

“Ina goyon bayan kiran da Majalisar Dattawa ta yi na a tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin takardun naira.

“Tun ba a je ko’ina ba jama’a sun fara shiga mawuyacin hali doriya a kan na matsalar tsaro da suke fuskanta.


“Jama’a suna cikin kunci, lamurra sun tabarbare saboda komai ba ya tafiya a kan tsari, kuma ya kamata Shugaban Kasa ya san halin da ake ciki,” a cewar Ortom.

Ba gudu ba ja da baya —CBN

Babban Bankin Najeriya CBN ya ce ba gudu ba ja da baya game da wa’adin da ya sanya na daina amfani da tsoffin takardun kudin kasar –N200, N500, da N1000 – daga ranar 31 ga watan Janairu.

Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele ne ya bayyana haka bayan ganawar Kwamitin Babban Bankin kan tsare-tsaren kudi a ranar Talata.

Mista Emefiele ya jaddada cewa babban bankin ya bayar da wadataccen lokaci ga ’yan kasar da su mayar da tsoffin kudadensu zuwa bankunan kasar domin musanya su da sabbi.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki