Posts

Showing posts with the label ATM

Hajj 2024: CBN Ya Janye Batun Biyan Kudin Guzurin Alhazai Ta Katin ATM

Image
Babban Bankin Najeriya ya dakatar da bayar da guzurin Alhazai na Hajji 2024 ta hanyar katin ATM Kwafin takardar da Bankin ya fitar wacce kuma  HAJJ REPORTERS ta gani mai kwanan wata 17 ga Mayu 2024 mai dauke da sa hannun daraktan riko na sashen ayyuka na kudi Solaja Muhammed J. Olawumi wanda aka aikewa bankunan kasuwanci ya ce “bayan gaggawar da aka samu tare da lura da karancin lokaci dangane da jigilar jirgin. Alhazan 2024, Shugabancin Bankin ya amince da biyan dukkanin tsabar kudi ga maniyyatan. “Ku lura cewa wannan sanarwar ta zarce tsarin da aka gabatar muku na farko na ayyukan Hajji na 2024. Nan ba da jimawa ba za a mika wata wasika a hukumance kan hakan.” Idan dai za a iya tunawa babban bankin ya sanar da hukumar alhazai ta kasa NAHCON da Jihohi da Rundunar Soji cewa za a biya kudin guzurin na Hajjin bana  wanda aka biya dala 500 ga kowane mahajjaci da kashi 60/40 cikin 100. tsabar kudi da kati Bankin ya ce dala 200 ne kawai za a ba da tsabar kudi yayin da za a ba da

Bankuna Za Su Fara Ba Da Katin Dan Kasa Mai Hade Da Na ATM —Pantami

Image
Gwamnatin Tarayya ta ba wa bankunan kasuwanci izinin fara ba wa abokan huldarsu katin cirar kudi na ATM da ke hade da katin shaidar dan kasa a wurin guda. Ministan Sadarwa mai barin gado, Isa Ali Pantami, ya sanar cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince bankuna su fara bayar da katin na bai-daya ba tare da sun caji kwastomomi ko sisi a kan kudin katin ATM da aka saba ba. “An ba wa bankuna izinin buga katunan Mastercard ko Visa da za su yi amfani a matsayin katin shaidar dan kasa ba tare da sun caji ’yan Najeriya karin kudi ba. “Duk mai son karbar katin banki, sai ya sanar da su cewa mai hade da katin dan kasa yake so, sai su ba shi kati daya da ya hade abubuwa biyun,” in ji Pantami. Ya bayyana cewa, Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) ta yi haka ne da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) “domin saukaka wa duk mai bukata samun katin dan kasa ta hannun bankinsa.” Da yake jawabi bayan zaman karshe na Majalisar Zartarwa ta Tarayya da gwamnatin Buhari ta gudanar, a