Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantun masu zaman kansu
Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu da na sa kai ta Jihar Kano (KSPVIB) ta dauki matakin rufe wasu makarantu guda takwas da ke aiki a fadin jihar, bisa dalilai na karya dokoki da kuma sabawa Æ™a’idojin gudanarwar hukumar. A yayinda yake ganawa da manema labarai, Shugaban hukumar Kwamared Baba Umar ya ce rufe makarantun ya zama wajibi saboda karya dokokin kara kuÉ—in makaranta da rashin yin takardun na izinin gudanarwa. Wadannan makarantu sun hada da: 1. Prime College Kano – Alu Avenue, Kano 2. Darul Ulum – Hotoro (Ahmad Musa Road) 3. Gwani Dan Zarga College – (Kofar Waika) 4. Awwal Academy – Rimi (Sumaila) 5. Dano Memorial College – (Sumaila) 6. Unity Academy – Wudil 7. Nurul Islam School 8. As-Saif College. A makon da ya gabata ne shugaban hukumar Baba Umar ya bada wa’adin mako biyu a kai korafin duk wata makaranta mai zaman kanta da ta kara kuÉ—in makaranta,Inda yace mutane sun bada hadin mai kuma su sun dauki matakin da ya dace na rufe irin wadannan makarantu tare da...