Yadda Dalar Amurka Ke Jefa ’Yan Nijeriya Cikin Kunci
Hauhawar farashin Dalar Amurka ya biyo bayan dokar da Shugaba Tinubu na barin Naira ta kwaci kanta a kasuwa. A ranar Litinin ta makon jiya ce Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu ta kai ziyara Jihar Kano domin kaddamar tsangayar karatun lauyanci na Jami’ar Maryam Abacha, wato MAUN. A lokacin ziyayar ce Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ba wa Remi Tinubu sako ta sanar da mijinta cewa, al’ummar Nijeriyar na cikin halin kaka-nika-yi, saboda haka ya yi abin da ya dace. Sai dai tun a farko, Uwagidan Shugaban Kasar ta yi kira ga mutanen Nijeriya da su kwantar da hankalinsu, inda ta tabbatar da cewa lallai akwai haske da nasara a gaba. Idan ba a manta ba, tun a jawabin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi lokacin rantsuwar karbar mulki, a ranar 29 ga watan Mayu ya bayyana cire tallafin man fetur, abin da ya haifar da karin kudin man nan take daga Naira 195 zuwa 540 a kan kowace lita daya. Sannan hauhawar farashin Dalar Amurka ya biyo bayan dokar da Shugaba Tinubu na barin Nai