An Sako Kannen Nabeehah Da Ke Hannun ’Yan Bindiga
Da misalin kare 12:30 na daren Asabar ne kannen na Nabeeh suka isa gidansu da ke Abuja, da rakiyar jami'an tsaro. Masu garkuwa da mutane sun sako ’yan uwan marigayiya Nabeeha Al-Kadriyah hudu da suka sace a Abuja bayan sun shafe kwanaki 19 a hannunsu. Da misalin kare 12:30 na daren Asabar ne kannen na Nabeeh suka isa gidansu da ke Abuja, da rakiyar jami’an tsaro. Kawunsu Sherifdeen, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho da safiyar Lahadi, “An sako ’yan matan ne da yammacin ranar Asabar kuma tuni sun nufi gida”. Su hudun su ne Najeeba ’ya aji 500 a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kanwartar da ke aji 300 a jami’ar Nadherah, tare da tagwayen kannensu, Habeeba da Haneesa. Dawowarsu bayan sun shafe kwanaki 19 a hannunsu ’yan bindigar da suka sace su a ranar 2 ga Janairu, 2024 ta sanya murna tskanin al’ummar unguwar. Sanarwar da Sherifdeen ya sanya wa hannu ta ce, “farin cikinmu game da dawowarsu ba zai misaltu ba, muna godi ga Allah da al’umma da suka ba mu gudunmawa. “Muna...