Posts

Showing posts with the label 'Yan Bindiga

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum Talatin Lokacin Sallah A Zamfara

Image
Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun mamaye masallacin ne da misalin karfe 5 na Asuba, a lokacin da ake shirin fara salla. Garba ya ce, “Za mu fara sallar asuba, kwatsam sai ’yan bindiga suka shigo masallaci suka umarci kowa ya fito ya bi su. “Kowa ya yi kokarin guduwa domin tsira amma suka tare ko’ina suka gargade mu cewa za su kashe duk wanda ya yi yunkurin guduwa. “Na samu na iya tsalle daga tagar kuma da sauri na shiga wani kango da ke kusa da masallacin na boye kaina,” in ji shi. Shaidan ya bayyana cewa ’yan bindigar sun bar baburansu a nesa da masallacin don kada a lura da motsinsu. Ya kara da cewa, “Daga baya sun tafi da mutanen zuwa inda baburansu suke, suka tafi da su.” A cewarsa, adadin mutanen da aka sace a masallacin zai iya wuce 30. Ya kara da cewa “masallacin ya cika a lokacin da suka kai hari kuma kadan ne daga cikin mu suka samu tsira.” Daya daga cikin shugabannin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bin diddigin ’yan bindiga...

An Sako Kannen Nabeehah Da Ke Hannun ’Yan Bindiga

Image
  Da misalin kare 12:30 na daren Asabar ne kannen na Nabeeh suka isa gidansu da ke Abuja, da rakiyar jami'an tsaro. Masu garkuwa da mutane sun sako ’yan uwan marigayiya Nabeeha Al-Kadriyah hudu da suka sace a Abuja bayan sun shafe kwanaki 19 a hannunsu. Da misalin kare 12:30 na daren Asabar ne kannen na Nabeeh suka isa gidansu da ke Abuja, da rakiyar jami’an tsaro. Kawunsu  Sherifdeen, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho da safiyar Lahadi, “An sako ’yan matan ne da yammacin ranar Asabar kuma tuni sun nufi gida”. Su hudun su ne Najeeba ’ya aji 500 a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kanwartar da ke aji 300 a jami’ar Nadherah, tare da tagwayen kannensu, Habeeba da Haneesa. Dawowarsu bayan sun shafe kwanaki 19 a hannunsu ’yan bindigar da suka sace su a ranar 2 ga Janairu, 2024 ta sanya murna tskanin al’ummar unguwar. Sanarwar da Sherifdeen ya sanya wa hannu ta ce, “farin cikinmu game da dawowarsu ba zai misaltu ba, muna godi ga Allah da al’umma da suka ba mu gudunmawa. “Muna...

'Yan bindigar da suka yi garkuwa da ni suna so su isarwa da gwamnati wani sake ne - Kanal 'Yandoto

Image
 

Hari Kan NSCDC: Kar Ku Raga Wa ’Yan Bindiga —Buhari Ga Sojoji

Image
  Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan jami’an Sibil Difens bakwai da wasu ’yan bindiga suka yi a Kaduna. Cikin wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar ranar Alhamis, Buharin ya bayyana takaicinsa da kisan jajirtattun jami’an da ya ce sun sadaukar da rayuwarsu ga Najeriya. “Jami’an NSCDC din da suka sadaukar da rayuwarsu wajen tsare kasarmu ba karamin jihadi suka yi ba a bakin aikinsu. “Ina jajanta wa iyalai da ’yan uwa da abikan arzikinsu. Ina rokon Ubangiji Ya ba su ikon jure wannan rashi”, in ji Buhari. Daga nan ne kuma shugaban ya umarci rundunar sojojin Najeriya da su kamo ’yan bindigar su yi maganinsu.

Gwamnatin Najeriya ta rufe tashar jirgin ƙasa a Edo bayan harin 'yan bindiga

Image
  Copyright: O Hukumomi a Najeriya sun sanar da rufe tashar jirgin Æ™asa ta Ekehen da ke jihar Edo, sa'o'i kaÉ—an bayan hari da 'yan bindiga suka kai tare da yin awon gaba da fasinjojin da ba a san adadinsu ba. Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da fasinjojin ke shirin hawa jirgin Æ™asan zuwa garin Warri da ke jihar Delta Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Edo Chidi Nwabuzor, ya ce kawo yanzu ba su samu labarin rasa rai ba. To sai dai ya tabbatar da cewa wasu fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga daga maharan. Ya ce 'yan bindigar É—auke da bindigogi sun far wa tashar jirgin Æ™asan da maraicen ranar Asabar, inda suka riÆ™a harbi a sama kafin su kama wasu da yawa daga cikin fasinjojin. Lamarin na zuwa ne Æ™asa da shekara guda bayan da 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan Æ™ungiyar Boko Haram sun kai hari kan jirgin Æ™asan Abuja zuwa Kaduna a arewacin Æ™asar tare da yin garkuwa da fasinjoji ma...

Labari da dumiduminsa : 'Yan bindiga sun sake yin garkuwa da fasinjojin Jirgin kasa

Image
Watanni bayan da ‘yan ta’addan suka kai hari tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama a cikin jirgin kasa zuwa Kaduna, wasu ‘yan bindiga sun kuma kai farmaki tashar jirgin kasa tare da kwashe mutane da yawa a Jihar Edo dake kudu maso kudancin Najeriya. Fasinjojin da suka samu raunuka, an ce suna jiran su hau jirgin kasa a wurin da lamarin ya faru, kafin su nufi garin Warri mai arzikin man fetur. Tuni dai hukumar 'yan sanda ta Rahotanni sun tabbatar da faruwar lamarin a cewar tashar talabijin ta TVC. Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce ‘yan bindigar da ke dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai farmaki tashar jirgin da misalin karfe 4 na yammacin ranar Asabar 7 ga watan Janairu, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su fito da shirinsu.  A ranar 28 ga Maris, 2022 ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da wasu fasinjoji. 2022 . Har yanzu dai Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya ba...

Kotun Senegal ta daure 'yan majalisa saboda dukan mace

Image
  Kotu a Senegal ta yanke hukuncin daurin watanni 6 a kan ‘yan majalisar dokokin kasar su biyu na bangaren 'yan adawa, saboda samun su da laifin dukar abokiyar aikinsu daga bangaren masu rinjaye. A ranar 1 ga watan Disambar da ya gabata ne dan majalisar dokoki Massata Samb ya yi dirar mikiya a kan wata ‘yar majalisar mai suna Amy Ndiaye, bisa zargin furta kalaman batanci a kan Moustapha Sy, shugaban wata jam’iyyar siyasa da ke cikin gungun ‘yan adawa sannan kuma shehin malamin addinin musulunci da ake mutuntawa a kasar. Wasu hotuna da ake rika yadawa sun nuna yadda Massata Samb ya lafta wa Amy Sy mari a cikin zauren majaliar ‘yayin da abokinsa dan majalisa Mamadou Niang ya sa kafa ya noshi matar a ciki bainar jama’a. Bayan faruwar wannan lamari, an kwantar da ‘yar majalisa Amy Sy a asibiti bayan da bayanai suka tabbatar da cewa tana dauke da juna biyu a lokacin faruwar lamarin, to sai dai a lokacin da yake yanke hukunci, alkali ya yi watsi da zargin yunkurin kisa kamar dai yad...

’Yan Bindiga Sun Sace Manoma 100, Sun Sanya Haraji A Neja

Image
  ’Yan bindiga sun kashe mutum hudu tare da yin garkuwa da mutum fiye da 100 ciki har dakanan yara a Kananan Hukumomin Rafi da Mashegu na Jihar Neja. Daga cikin wadanda bata-garin suka kashe har da basaraken gargajiya da ’yan banga biyu da wani mutum daya a Karamar Hukumar Mashegu. Maharan sun kuma sanya harajin Naira miliyan uku-uku domin dakatar da garkuwa da mutane a yankunan kananan hukumomin Rafi da Shiroro inda suka yi awon gaba da mutum 61. Al’ummar yankunan Rafi da ’yan bindiga suka kai wa hari sun shiga yin kaura zuwa wasu wurare domin samun aminci. Rahotanni sun bayyana cewa a mako uku da suka gabata mahara sun far wa kauyuka 14 a kananan hukumomin, inda suka sace yawancin mutanen a gonakin wake,  marasa da dawa. Wani mazaunin yankin ya ce sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron kada a yi garkuwa da su, a yayin da ’yan bindiga ke sace masu amfanin gona. 'Yan Bindiga Garkuwa noma