Posts

Showing posts with the label Masallaci

An Kama Matashin Da Ya Banka Wuta Ga Masu Sallah A Masallaci

Image
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar cewa binciken farko ya nuna matashin ya yi wannan aika-aika ne a sakamakon rikicin gado. Aminiya ta ruwaito cewa an banka wa mutane wuta a lokacin da suke sallar Asuba a wani masallaci da ke kauyen Larabar Abasawa da ke Karamar Hukumar Gezawa a ranar Laraba. Shaidu sun ce sai da wanda ake zargin ya shiga masallacin ya rurrufe kofofin ya zuba makamashi ya kyasta wuta sannan ya kulle su a ciki ya tsere. “Da kyar mutanen da suke waje suka yi nasarar balle kofar su ceto na cikin masallacin,” in ji wani mazaunin yankin. Wani dattijo da ke salla a masallacin ya ce sai da aka yi raka’a daya an ffara raka’a ta biyu wanda ake zargin ya sa wutar. Malamin wanda ya ce ba da shi aka fara sallar ba saboda ya makara, ya bayyana yadda mutane suka kokkone a masallacin, kuma akasarin wadanda suka konen dattawan garin ne. Majiyarmu ta samu bayani cewa akalla mutane 28 ne suka samu mummunan kuna a sakamakon wutar da mutumin ya cimma a masallacin fa ke