Posts

Showing posts with the label Tsabar kudi

An haramta cire tsabar kudi daga asusun Gwamnati

Image
Hukumar da ke sanya ido kan hada-hadar kudade a Najeriya (NFIU) ta haramta cire tsabar kudi daga asusun Gwamnatin Tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi daga ranar 1 ga watan Maris, 2023. NFIU ta ce daga ranar, laifi ne a biyan ma’aikatan gwamnati alawus-alawus din tafiyar aiki a cikin gida ko zuwa kasashen waje da tsabar kudi. An gano gawar mutum 16 a hatsarin jirgi a Kebbi ’Yan sanda sun cafke ’yan daba 63 a taron Tinubu a Kano Babban Daraktan hukumar, Modibbo Tukur, ne ya bayyana haka a Abuja ranar alhamis, inda ya ce karin wasu sabbin tsare-tsaren na tafe. Ya ce za a fara amfani da sabbin tsare-tsaren ne bayan fara aikinsa dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) na takaita cirar tsabar kudi ga daidaikun mutane da kamfanoni a Najeriya. Da yake karin haske kan dokokin, Modibbo ya ce hakan yayi daidai da sashi na 3(1)a-s, da sashi na 23(2) na kundin hukumar. A baya dai bisa dalilai daban-daban, ma’aikatun gwamnati da hukumomi, na fitar da kudade daga bankuna don yin mu’amal...