Na Cika Alkawuran Da Na Daukar Wa ’Yan Najeriya – Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya cika alkawuran da ya dauka na yaki da ’yan ta’addan boko Haram da farfado da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
A cewar Kakakin Shugaban, Femi Adesina, Buhari ya bayyana hakan ne yayin wanin taron cin abinci da aka shirya domin karrama shi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Giwa ta kashe manomi a Uganda
’Yan bindiga sun harbe jami’an tsaro 12 a Kaduna
Shugaban dai ya fara ziyarar yinin biyu ne a Jihar ranar Litinin.
Sanarwar ta kuma ce Shugaban ya bigi kirjin cewa babu wanda zai zarge shi da tara dukiyar da ba ta halas ba lokacin da yake mulki, inda ya ce ko taku daya ba shi da shi a wajen Najeriya.
A wani labarin kuma, Shugaban ya ce babu wata kungiyar ’yan ta’adda da ta isa ta wargaza Najeriya.
Shugaban Kasar ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara fadar Sarkin Damaturu, Alhaji Hashumi Ibn Elkanemi II a fadarsa da ke garin Damaturu, ranar Talata.
Buhari ya kuma bukaci ’yan Najeriya da su kara kaimi tare da ba da karfin gwiwa ga hukumomin tsaro kan kokarinsu na zaman Najeriya kasa daya dunkulalliya.
“A watanni hudu masu zuwa, in na bar mukamin Shugaban Kasa, zan ci gaba ne da dagewa, kuma ina fatan zan aiki lafiya.”
“Dole ne mu samar da kwarin gwiwa a kasarmu tare da tabbatar da cewa ba mu kawo cikas ga tsaro ba ta kowace fuska domin tsaro da tattalin arziki su ne mafi muhimmanci ga kowace kasa.
“Mun sha fama da yawa wajen hada kan kasar nan, kuma ina rokon ku da ku dage da tabbatar da cewa ba za mu bari wani ya sake wargaza mu ba,” in ji shi.
Shugaban ya kuma bayyana farin cikinsa da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Yobe da ma yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ya gode wa Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni da takwaransa na jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, bisa jajircewar da suka yi na sake gina makarantu, cibiyoyin lafiya da cibiyoyin da ’yan ta’addan suka lalata.
Shugaban ya ce, ya lura da cewa ‘’da gangan aka yi yunkurin ruguza Najeriya amma Allah bai yarda ba,’’ ya kara da cewa ‘’Allah ya taimaki Najeriya ta dawo.
Ya kuma yabawa jami’an soji da ‘yan sanda bisa sadaukarwar da suke yi wajen kare Kasar nan daga fadawa cikin mummuna yanayi.
Shugaban ya kara da cewa, da suka yi yaki don kare hadin kan Najeriya a lokacin yakin basasa, wadanda ke cikin wannan kwarewa ba za su taba barin wani ya sake ruguza kasar nan ba
Da ya ke jawabi, Gwamna Buni ya shaida wa Shugaban Kasar cewa, a cikin wannan yakin da ake yi da ’yan tada kayar baya, ’yan ta’adda sun taba mamaye hatta fadar Sarkin Damaturu a baya.
Sai dai ya ce tun bayan zuwan gwamnatin APC a 2015, Jihar ta samu sa’ida.
Shi kuwa Sarkin na Damaturu ya mika godiyarsa ga Shugaban Kasar kan inganta harkokin tsaro a kasar, inda ya ce, “Mun sha wahala a baya, amma gwamnatinka ta hada kan kasa cikin ikon Allah.”
(AMINIYA)