Posts

Showing posts with the label Hukumar NDLEA

’Yan Kasuwa 2 Sun Yi Kashin Kunshi 193 Na Hodar Iblis A Hannun NDLEA

Image
Wasu ’yan kasuwa biyu sun yi kashin kunshi 193 na Hodar Iblis bayan shafe kwanaki uku a hannun jami’an Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA). Bayanai sun ce an cafke ababen zargin biyu ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, a ranar 10 ga watan Mayu yayin shigowarsu Najeriya daga kasar Uganda. Haaland ya zama dan kwallon da babu kamarsa a Firimiyar Ingila a bana Angola ta zarce Najeriya a hako danyen man fetur —OPEC Mai Magana da Yawun NDLEA, Femi Babafemi ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Lahadin. Mista Babafemi ya ce an dade ana neman mutanen biyu ruwa a jallo wadanda ake zargi ba su da wata sana’a face safarar miyagun kwayoyi. Ya bayyana cewa bayan shafe kwanaki a hannun hukumar, daya daga cikinsu ya yi kashin kunshi 100 na Hodar Iblis wanda nauyinta ya kai kilo 2.137, yayin da abokin tafiyarsa ya yi kashin kunshi 93 na hodar mai nauyin kilo 1.986. Kazalika, jami’an NDLEA sun kai samame wata mashayar miyagun kwayoyi