Posts

Showing posts with the label zaben shugabannin majalisa

APC za ta yi zaman gaggawa kan shugabanci a majalisar dokokin Najeriya

Image
  A ranar Laraba 10 ga watan Mayu ne kwamitin gudanarwa na jam`iyyar APC zai yi wani zaman gaggawa kan rikicin neman shugabanci a majalisar dokoki ta goma da za a kafa. A farkon makon nan ne jam'iyyar ta fitar da wata sanarwa da ke nuna ta kebe shugabancin Majalisar Dattawa da ta Wakilai ga wasu shiyyoyin kasar. A sanarwar, APC ta ware wa shiyyar Kudu Maso Kuduncin Najeriya kujerar Shugaban Majalisar Dattawa tare da ayyana sunan Sanata Godswill Akpabio a matsayin wanda zai rike wannan mukamin. Sai kuma kujerar Kakakin Majalisar Wakilai wacce jam'iyyar ta bayyana sunan Tajudeen Abbas daga shiyyar Arewa maso Yammacin kasar. Bisa ga dukkan alamu wannan matakin na jam'iyyar bai yi wa wasu 'ya'yanta dadi ba lamarin da ya sa wasu daga cikinsu yunkurin bijire mata. Wannan hali da ake ciki ne zai sa kwamitin gudanarwa na jam`iyyar ta APC ya gudanar da zaman gaggawar domin nemo bakin zaren warware matsalar. Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano tuni wasu masu takarar kujera