Zan Kammala Aikin Tashar Jiragen Ruwa Ta Baro Idan Kuka Zabe Ni – Atiku
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin kammala aikin tashar jiragen ruwa ta Baro da ke Jihar Neja, muddin aka zabe shi a zabe mai zuwa. Atiku ya kuma ce jam’iyyarsa ce kawai take da siddabarun da za ta magance kalubalen tsaro da ya addabi kasar, musamman ma Jihar Neja. Burkina Faso ta ba sojojin Faransa wata daya su fice daga kasarta Ya yi wadannan alkawuran ne lokacin da yake jawabi ga wasu kusoshi da magoya bayan jam’iyyar a Minna, babban birnin Jihar Neja ranar Asabar. Atiku ya ce PDP ce ta faro aikin na Baro rimi-rimi lokacin da take mulki, amma APC na zuwa ta yi watsi da shi. A cewar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, “Muna addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya a Jihar nan. Kun san PDP ce kawai za ta iya dawo da zaman lafiya a Neja. Lokacin da take mulki daga 1999 zuwa 2015, akwai matsalar tsaro a Neja? Muna so mu tabbatar muku cewa muddin PDP ta dawo, matsalar za ta zama tarihi. “Muna kuma so mu tabbatar muku cewa aikin tashar Ba...