Search This Blog

Showing posts with label Laminu Rabi'u Danbappa. Show all posts
Showing posts with label Laminu Rabi'u Danbappa. Show all posts

Tuesday, 7 May 2024

Hukumar Alhazai Jahar Kano Ta Biya Sama Da Naira Biliyan 18 Ga NAHCON Domin Hajin Bana

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana a yau cewa hukumar ta aikawa hukumar alhazai ta kasa sama da Naira biliyan 18 domin shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin shekarar 2024. 

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa duk da cewa mutane 3,110 ne suka biya kudin aikin hajji, amma da yawa suna jiran bizarsu daga hukumar alhazai ta kasa. 
Ya kuma bukaci hukumar da ta hanzarta bayar da bizar kafin rufe ranar, inda ya jaddada kudirin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na kammala gyara a sansanin Alhazai kafin a fara jigilar maniyyata. 

Darakta Janar din ya kara da cewa, ba kamar shekarar da ta gabata ba, a  wannan shekarar gwamnati ta samar da dukkan kayayyakin da ake bukata a sansanin Alhazai  gabanin gudanar da aikin hajji domin amfanin Maniyyata 

Da take jawabi, Hajiya Rabi D’nyako Jami'ar gudanarwa a ofishin hukumar alhazai ta kasa dake Kano, ta bayyana kudurinta na magance korafe-korafen biza inda nan take ta gabatar da takardar tambayoyi ga hukumar alhazai. 
A nasa jawabin shugaban hukumar alhazai ta Kano, Alhaji Yusif Lawan ya mika godiyarsa ga hukumar alhazai ta kasa bisa wannan ziyara da suka kai musu, inda ya bayyana cewa ta zo a kan lokaci. 
Alhaji Yusif Lawan ya kuma yabawa ofishin hukumar alhazai ta kasa na Kano bisa hadin kan da suke bawa Hukumar Alhazai ta Kano 

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...