Gwamnatin Soja ta fi ta farar hula tausayin malaman Jami'a - ASUU

Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce gwamnatocin mulkin soja na baya a Najeriya sun fi ta farar hula mai ci a yanzu tausayin su.

Ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Abuja, yayin kaddamar da wasu littattafan manyan makarantu guda 50 da wasu marubuta suka wallafa.

Hukumar da ke Kula da Manyan Makarantu ta Najeriya (TETFund), ce dai ta dauki nauyin wallafa littatafan.

A cewar Shugaban, “A shekarar 1992, lokacin da muka yi yajin aiki, sai muka bukaci a kalubalance mu, mu kawo mafita kan yadda za a samo kudaden da za a aiwatar da yarjejeniyoyin da aka amince da su.


“Haka aka yi kuwa suka kalubalanci ASUU, inda ko kwana uku ba a yi ba muka kawo batun kafa TETFund, wacce kuma gwamantin mulkin soja ta wancan lokacin ta amince. Ni ina ga gwamnatin soja ta ma fi ta farar hula tausayinmu.

“Yadda aka yi aka sami hukumar TETFund ke nan. An rattaba hannu a kan kudurin ya zama doka a 1993. Sai da ASUU ta sake komawa yajin aiki a karo na uku kafin a fara fitar wa TETFund kudi,” inji Shugaban na ASUU.
Dangane da matakin “babu aiki babu albashi” na Gwamnatin Tarayya da ya kai ga malaman suka shafe wata takwas suna yajin aiki a bara kuwa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya roki ’yan Najeriya da su dada matsa wa gwamnati lamba ta ceto manyan makarantun kasar daga durkushewa.

Shi ma da yake jawabi yayin kaddamar da littattafan guda 50, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya ce sabbin littattafan za su rage kaka-gidan da na ketare ke yi a manyan makarantun kasar.


Adamu, wanda Minista a Ma’aikatar Ilimi, Goodluck Nanah Opiah ya wakilta, ya ce an yi lokacin da kusan dukkan makarantun Najeriya suka ta’allaka da na ketare, duk kuwa da makudan kudaden da ake kashewa wajen musayar kudade kafin sayo littattafan.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki