Posts

Showing posts with the label Faransa

Tinubu Ya Gana Da Ganduje A Abuja

Image
  Shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya gana da Gwamnan Jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje a gidansa na Defense House da ke Abuja. Da yammacin Asabar É—in nan dai Ganduje ya shiga sahun waÉ—anda suka taro Asiwaju Tinubu lokacin da ya sauka Abuja daga Æ™asar Faransa. Bayan an isa gida kuma sun yi ganawar sirri tsakaninsu. Ganawar dai ba ta rasa nasaba da Æ™orafin da Ganduje yake da shi game da ganawar Asiwaju Tinubu da tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a birnin Paris. A baya-bayan nan dai aka ji wani sautin hirar wayar tarho na yawo inda Ganduje ke kukan zaÉ“aÉ“É“en shugaban Æ™asar bai kyauta masa ba da ya yi wannan tattaunawar. Kawo yanzu dai Ganduje bai bayyana wa manema labarai matsayar da suka cimma da Asiwaju Tinubu ba . AMINIYA