Posts

Showing posts with the label Zaben 2023

Darussa Daga Siyasar Kano Ta 2023 - Dr Sa'idu Ahmad Dukawa

Image
Tun lokacin da Injiniya Abba Kabir Yusuf ya zama gwamnan Kano daga zaben da aka gudanar a watan Maris na wannan shekarar (ta 2023) har izuwa ranar Laraba, 20/9/23, siyasar Kano (wacce ake yiwa taken “sai Kano!”) ta dada zafafa fiye da ko da yaushe a wannan zubin dimokaradiyyar (ta Jamhuriya ta hudu). A bisa fahimtata, dalilai kamar shida ne suka janyo haka.  Za mu yi bitarsu a takaice domin amfanin gaba. 1. Zafin hamaiyar siyasa tsakanin Senator Rabiu Musa Kwankwaso da Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Wannan ta sa wadannan jagororin na Kano guda biyu sun fifita bukatun kansu, na neman wani ya ga bayan wani a siyasance, fiye da bukatar da Kano take da ita na su hada kansu domin su samarwa da Kano zaman lafiya da cigaba mai dorewa.  A dalilin haka magoya bayansu sun dukufa wajen ganin jagoransu ne a sama ta kowane hali. Don haka cece-kuce ya kazanta a tsakanin juna. Da Allah zai sa idan aka kai karshen tirka-tirkar wadannan manyan biyu su yafewa juna su yi sulhu a tsakaninsu da za

Alhassan Doguwa ya yi tazarce a karo na hudu

Image
  Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya Alhassan Ado Doguwa ya ci zabe a karo na biyar. Baturen zaben da aka kammala a ranar Asabar, Farfesa Sani Ibrahim, ya ce Alhassan Ado Doguwa ya yi nasarar komawa kan kujerarsa ne bayan ya samu kuri'u 41,573 a yayin da dan takarar jam'iyyar NNPP, Yusha'u Salisu, ya zo na biyu da kuri'u 34,831. Idan za a iya tunawa bayan zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Maris, INEC ta bayyana Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara. Amma daga bisani aka janye nasarar Doguwa bayan da baturen zaben, Farfesa Ibrahim Yakasai ya cewa tursasa masa bayyana sakamakon aka yi, don haka bai samu nutsuwar yin lissafin kuri'un da aka jefa yadda ya kamata ba, kasancewar rayuwarsa da ta ma'aikata na cikin hadari a lokacin. Amma daga baya da aka yi lissafi aka gano zaben bai kammalu ba saboda kuri'un da aka soke sun zarce tazarar da ke tsakanin kuri'un Doguwar da na Yusha'u. Hakan ne ya sa aka kammala zaben a yau, wanda Alhassan Ado Dogu

Zababben Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf na ya al'ummar Kano domin su Karbar Shaidar Cin Zabensa

Image
Zababben Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida Gida yana gayyatar dumbin magoya bayansa, mambobin jam'iyyar NNPP da kuma manyan masu ruwa da tsaki, zuwa gabatar da takardar shaidar cin zabe ga dukkan 'yan takarar da suka ci zabe a ranar Asabar 18 ga wata. Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a Kano ta shirya ranar Laraba 29 ga Maris, 2023 da karfe 10 na safe a sakatariyar INEC don bayar da shaidar cin zabe ga zababben gwamna da mataimakinsa da ‘yan majalisar jiha. Kakakin zababben gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, a wata sanarwa a ranar Talata ya ce za a gudanar da taron ne a dakin taro na INEC da karfe 10:00 na safe. Ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar NNPP da duk wadanda aka gayyata, wadanda suka shahara da son zaman lafiya da bin doka da oda, da su rika gudanar da harkokinsu cikin tsari a lokacin bikin da kuma bayan bikin, tare da yi wa kowa fatan alheri. SABATURE

Sufeto Janar Ya Sake Turo Usaini Gumel A Matsayin Sabon Kwamishinan 'Yan Sanda Na Kano

Image
Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali, ya sake soke turo kwamishinan ‘yan sandan Kano. A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, Sufeto Janar din ya soke aika Feleye Olaleye a matsayin kwamishinan ‘yan sandan Kano tare da sanya CP Ahmed Kontagora a matsayin wanda zai maye gurbinsa. Sai dai a wata siginar da aka sake fitarwa a daren jiya, sufeto janar din ya nada CP Usaini Gumel a matsayin wanda zai jagoranci rundunar 'yan sanda ta Kano lokacin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a jihar. A ranar 8 ga Maris, bayan zanga-zangar da ‘yan adawa suka yi, IGP ya sauya matakin da aka tura CP Balarabe Sule, tsohon babban jami’in tsaro ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a matsayin wanda zai maye gurbin CP Mohammed Yakubu A cikin sabuwar takardar da aka fitar mai dauke lamba TH.5361/FS/FHQ/AB3/SUB.6/146, Mista Alkali kuma ya sake yin wasu Æ™ananan canje-canje a cikin umarnin. IGP ya umurci DCP Auwal Musa da ya karbi DCP Nuhu Darma a matsayin mataimakan kwamishin

2023: Idan Na Zama Gwamna Zan Bawa Kananan Hukumomin 'Yancinsu - Gawuna

Image
Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar  APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi alkawarin baiwa kananan hukumomin jihar ‘yancin cin gashin kansu idan aka zabe shi a matsayin gwamna. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da shirin gidan talabijin na NTA cikin shirin "The Balot". "Ƙananan Hukumomin wani bangare ne na gwamnati kuma su ne matakin kusa da jama'a wanda ke taimakawa hatta ci gaba da rarraba albarkatu da ayyuka". "A matsayina na tsohon shugaban karamar hukumar na san abin da ya shafi gudanar da mulkinta". Lokacin da nake shugaban karamar hukuma, an ba ni cikakkiyar dama nayi  aiki. Hakan ya sa muka samu nasarori da dama don haka idan aka zabe mu a matsayin Gwamna zan mayar da martani kamar yadda Gawuna ya bayyana”. A sanarwar da babban sakataren yada labaransa, Hassan Musa Fagge ya fitar, Gawuna Ya kara da cewa shi ne wanda ya fi cancanta kuma a shirye ya ke ya zama Gwamnan Jihar Kano bayan ya yi aiki

Zamu Kalubalanci Zaben Shugaban Kasa - Atiku Abubakar

Image
ÆŠan takarar shugaban Æ™asa na babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, Atiku Abubakar ya ce dole ne kowa ya Æ™alubalanci zaÉ“en da aka yi na ranar 25 ga watan Fabarairu. A taron manema labarai da ya gabatar a Abuja, tsohon mataimakin shugaban Æ™asar ya ce, abin da ya faru a kan zaÉ“en fyaÉ—e ne aka yi wa dumukuradiyya. Atiku ya ce, a tarihin Æ™asar wannan shi ne zaÉ“e mafi muni da aka taÉ“a yi, wanda kuma dama ce ta sake daidaita Najeriya. Amma kuma hukumar zaÉ“en Æ™asar, INEC ta lalata tare da watsa wannan dama da buri na ‘yan Najeriya. ÆŠan takarar na PDP, ya ce zaÉ“en ya kasa kaiwa matsayi da matakin da aka sa rai zai kai. Sannan ya ce lauyoyinsu suna duba lamarin kafin su san matakin da za su É—auka na gaba. Ya ce idan har ya je kotu ba a yi masa adalci ba to zai bar su da Allah. Za mu kawo muku karin bayani a nan gaba. BBC 

Kotun Magistare A Kano Ta Aike Da Alasan Ado Doguwa zuwa Gidan Kaso

Image
Kotun Magistare dake Kano, ta aike da shugaban masu rinjaye na majalisar Wakilai, Alasan Ado Doguwa zuwa gidan kaso kafin ta bayar da belinsa.  SOLACEBASE  reports that the defendant, Alhassan Doguwa is standing trial on several offences that include, criminal conspiracy, culpable homicide, unlawful possession of fire arm, mischief and public disturbance Babban Alkalin Kotun, Ibrahim Mansur Yola, shi ne ya aike da wanda ake zargin har zuwa ranar 7 ga watan Mayu, lokacin da za a saurari batun Karbar belinsa 

Zabe - Gawuna Ya Taya Zababben Shugaban Kasa Tinubu Murna

Image
Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya taya zababben shugaban kasa Sen.Bola Ahmed Tinubu da mataimakin zababben shugaban kasa Sen.Kashim Shettima murnar nasarar da suka samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar. 25 ga Fabrairu, 2023.   "Ni da kaina da abokina Hon.Murtala Sule Garo ina muku fatan nasara yayin da kuke daukar nauyin sabunta fata tare da addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya kara muku hikima, karfi, jagora da jagora don aiwatar da aikin da aka dora muku".   "Jagaban, kai ne mutumin da ya dace a halin yanzu, nasararka nasara ce ga dimokuradiyya, ka yi aiki tukuru domin samun nasarar jam'iyyarmu ta APC."   "Ka tabbatar da cewa kai dan dimokradiyya ne na gaske wanda ya nuna jajircewa, kishi da sadaukarwa ga hidima da ci gaban kasarmu."   "Mun gode muku bisa jajircewarku da tsayin dakanku domin mun yi imanin cewa kuna da kyakkyawar niyya don cika alk

Nasarar Tinubu Ta Yi Nuni Da Yadda Dimokwaradiyya Ta Yi Aikinta - Ganduje

Image
Gwamna Ganduje ya bayyana Nasarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2023, a matsayin shugaban kasa a Najeriya, ta nuna yadda aka yi dimokaradiyya ta gaskiya.  A wani martani ga nasarar da Tinubu ya samu, Gwamna Ganduje ya yaba da gwagwarmayar siyasa da jajircewar daular siyasar Tinubu, wadda ta samar da wasu abubuwa daga ko’ina a fadin kasar nan, wajen tabbatar da cewa dan takarar shugaban kasa ya yi nasara baki daya. “Sahihancin jarin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a kan É—an adam, ci gaban Æ™asa da haÉ—in kan Æ™asa ya taka muhimmiyar rawa wajen fifita shi ga dukkan sassan Æ™asar,” in ji shi. Ya kara da cewa, “Yakin da Tinubu ya kwashe shekaru da dama yana yi na maido da mulkin dimokuradiyya a kasar nan, ‘yan Najeriya sun fahimta sosai. Don haka, muna ganin hikima da kuma dalili mai kyau na jinginar da makomarmu gare shi.” Yayin da yake tabbatar da cewa, zababben shugaban kasar zai bullo da dabarun tunkarar matsalolin da suka addabi al’um

Hukumar DSS Ta Kama Alasan Ado Doguwa

Image
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Dogowa, saboda zargin kisan wasu magoya bayan jam’iyyar adawa a yankin.  Majiyarmu ta rawaito cewa an kama Doguwa ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano , a kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin umarah a ranar talata.  Kamen ba zai rasa nasaba da kisan da aka yi wa magoya bayan ‘yan adawa kusan 15 a karamar hukumar Tudunwada a lokacin zaben da aka kammala ba .  Rahotanni sun ce an kulle wasu daga cikin mutane a wani gini inda aka kona su kurmus, lamarin da ya sa aka gagara kubutar Kadaura24 

Take-Taken Da Ake Nufi Da Karancin Mai Da Sauya Fasalin Naira —Tinub

Image
Dan takarar Shugaban Kasa karkashin Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin matsalar karancin mai da ake fuskanta da sauya fasalin wasu takardun Naira da aka yi, take-taken neman wargaza Zaben 2023 ne kawai. Tinubu ya bayyana haka ne yayin gangamin yakin neman zaben APC da ya gudana ranar Laraba a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun. Na tafka kuskure a tafiyar Buhari, ba zan maimaita da Tinubu ba — Naja’atu Muna da hujjoji kan cewa Tinubu tsohon mai laifi ne – Dino Melaye  “Ba sa son zaben ya gudana. So suke su wargaza shi. Za ku bari hakan ta faru?, in ji Tinubu. Dan takarar ya ce yana da yakinin matsalar karancin fetur ba za ta hana ’yan Najeriya zuwa kada kuri’a ba ranar zabe. “Sun fara bullo da batun ‘babu mai, kar ku damu, idan babu mai za mu taka da kafa zuwa wajen zabe. “Idan kun ga dama ku kara kudin mai, ko boye man ko kuma ku canza wa naira launi, za mu ci zabe,” in ji shi.

Idan Mijina ya Gza bayan Shekara hudu, Ka da ku Sake Zabarsa - Matar Tinubu

Image
  Mai dakin dan takarar Shugaban Kasa na jam ’ iyyar APC, Sanata Oluremi Tinubu, ta shawarci  ’ yan Najeriya da kada su sake zaben mijinta a karo na biyu idan ya gaza tabuka komai bayan shekara hudu. Oluremi ta yi wannan kira ne a wajen gangamin yakin neman zaben Tinubu/Shettima na matan shiyyar Kudu maso Gabas wanda ya gudana a Owerri, babban birnin Jihar Imo. Ta ce, “A ajiye batun addini a gefe, ni Kirista ce. Ko kun taba tunanin cewa wata rana za a samu ‘yan takara Kirista da Kirista? “Me ya kamata ya zama madogara? Tun da mun jarraba ‘yan takara Musulmi da Kirista, bari mu jarraba wannan ma mu gani sannan bayan shekara hudu idan ba su tabuka komai ba kuna iya yin waje da su,” in ji ta. Ta kara da cewa, bai kamata addinin mutum ya zama abin damuwa a sha’anin zabe a Najeriya ba, maimakon haka kamata ya yi a yi la’akari da tsoron Allah da dan takara ke da shi. Saboda a cewarta, “Idan ana da mutum mai tsoron Allah, ba wai Kirista ko Musulmi ba, amma dai mutum mai tsoron Allah. Idan mai

Kuyi amfani da kalaman da al'uma zasu gamu dasu wajan yakin neman zabe: Mai Martaba Sarkin Kano.

Image
Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ad Bayero ya yi kira ga masu neman kujerun mulkin kasar nan da su tabbatar sunyi kalamai da al'umma za su gamsu da su wajen neman kuri'ar alumma a zaben shekarar 2023. A sanarwar da Sakataren yada labaran Masarautar Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya sanyawa hannu, ta ce Sarkin ya bayyana haka ne lokaci da dan takarar shugaban kasa na jam'iyar SDP Adewale Adebayo da dantakar kujerar gwamnan jihar Kano Dr. Muhammad Bala gwagwarwa yayin da su ka  ziyar ce shi a fadar sa. Alhaji Aminu Bayero, ya kuma nemi da duk wani dake neman kujerar da yasan cewa Allah ne ke bayar da Mulki bawai karfin ikon tada zaune tsayeba. Da yake nasa jawabin, dan takarar Gwamna na jam'iyyar ta SDP Bala Muhammad Gwagwarwa ya ce sun ziyarci fadar sarkin ne domin neman tabaraki da addu'ar. A wani cigaban kuma Martaba Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nada Dr. Malam Umar Ibrahim Indabawa  a matsayin sabon limamin  Masallacin Darul hadis dake Ung

2023: Amurka Za Ta Mara Wa Najeriya Baya A Harkar Zabe

Image
Gwamnatin Kasar Amurka ta ce za ta mara wa Najeriya baya dangane da zaben 2023 don tabbatar da masu kada kuri’a sun samu aminci a yayin zaben. Amurka ta bayyana hakan ne ta bakin ofishin jakadancinta a Najeriya. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito Amurka za ta mara wa kasar baya ne karkashin shirin ‘Vote023’. Vote023 shiri ne na musamman don wayar da kan jama’a kan harkokin zabe musamman ganin yadda zaben 2023 ya karato. Daya daga cikin jagororin shirin ‘Vote023’, Misis Angela Ochu-Baiye ce ta bayyana haka ranar Asabar a Legas. Ochu-Baiye ta ce abin a yaba ne ganin Ofishin Jakadancin Amurka ya amice su yi aiki tare don wayar da kan ’yan kasa kan zaben 2023.