Posts

Showing posts with the label Asibitin Malam

Hukumar Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ta yi Allah wadai kan sakacin da wani likita ya yi lokacin da yake kula da lafiyar wani jariri

Image
  Jaririn wadanda aka haifa makon da ya gabata ya zo da wata matsala wadda ta bukaci yi masa gwaji ta hanyar daukar jininsa a inda likitan ya shiga dimuwa wanda ya haifar da abin da ya faru. A cikin sanarwar da shugabar sashen hulda da jama’a ta Asibitin Hajiya Hauwa Muhammad Abdullahi ta sanyawa hannu, Hukumar Asibitin ta girgiza da Jin Wannan mugun labari Wanda a shekaru  talatin da uku da kafuwar Asibitin Hakan bai tabar faruwa ba.  Hukumar tana jajentawa iyayen wannan jariri bisa ga abin da ya faru. A Kuma halin da ake ciki an mika wa kwamitin da yake bibiyar matsalolin badakala da sakacin aiki wato (Committee on Negligence of Duty)domin yin zurzurfan bincike tare da daukan mataki akan duk Wanda yake da hannu a cikin wannan sakaci da ya faru. Shugaban Asibitin Koyarwan farfesa Abdurrahman Abba Sheshe ya yi kira ga duk Maras lafiya ko Yan Uwan marasa lafiyan da su ga ba su gamsu da yadda ake kula da lafiyar su ko ta Yan Uwansu ba ,da su gaggawa wajen sanar da hukumar Asi