Shugaban NAHCON Ya Ziyarci Ofishin Jakadancin Saudiyya na Abuja.
Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya wato NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya kai ziyarar ban-girma zuwa ofishin Huldar Jakadanci na Saudiyya inda ya gana da Jakadan Saudiyya dake Abuja, Ambasada Faisal Ibrahim Al-Ghamidy, a ranar Laraba A sanarwar da Hukumar ta fitar ta ce, Shugaban ya kai ziyarar ce da nufin bunkasa dangantaka da habakar da hadin-gwiwa tsakanin bangarorin biyu. Malam Arabi ya jaddada jin dadinsa ganin yadda Jakadan Kasar Saudiyya Ambassada Faisal ke bada cikakken goyon-baya ga Hukumar da tareraya irinta Huldar Jakadanci karkashin Ofishin Jakadancin Saudiyyar. Sanarwar tace ziyarar, ta bayyana karara yadda dadaddiyar alaqa ta jituwa ke tsakanin NAHCON da Ofishin Jakadancin Saudiyyar, abinda ke nuni da fahimtar-juna da hadin kai dake wanzuwa a tsakanin Kasashen biyu. A Yayin ganawar, bangarorin biyu sun zanta batutuwa masu ma’anar gaske, abunda ke tabbatar da muhimmancin tarayyarsu wajen kara inganta gudanar da Al-amurran A...