Babban Bankin Najeriya Ya Ce Ya Kashe Dalar Amurka Biliyan 11.42 Don Farfado Da Darajar Naira

Rahoton da babban bankin Najeriya ya fitar a shafinsa na yanar gizo ya ce bankin ya kashe dalar Amurka biliyan 11.42 a cikin watanni 7, daga watan Janairu zuwa watan Yuli na shekarar 2022 domin a farfado da darajar naira.

Masana tattalin arziki da kwararru a fannin hada-hadar kudi na ganin wannan kokari da bankin CBN ya yi bai hana matsalar canji tsakanin dalar Amurka da naira ba, hasali ma har yanzu farashin kayan masarufi na karuwa a kasuwanni.

Ya zuwa wannan lokacin, ana sayar da dalar Amurka daya a kan naira 750 a kasuwar bayan fage yayin da a banki kuma ake sayar da dalar kan naira 450, bambancin naira 300 kenan tsakanin banki da kasuwar bayan fage.

A hirar shi da Muryar Amurka, Umar Garkuwa, daya daga cikin manyan ‘yan canjin kudi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya ce karyewar naira laifin babban bankin kasar ne ba laifin ‘yan canji ba.

Garkuwa ya ce matsalolin harkar canji a Najeriya ba kamar a wasu kasashen duniya ba ne, domin lamarin ya zama wata harka da wasu ‘yan kasar da kuma CBN suke amfani da ita wajen azurta kansu. Ya kara da cewa, kasuwar canjin kudin kasashen waje a Najeriya dabam ta ke kuma babu yadda za a magance 

A lokacin da shugaba Mohammadu Buhari ya karbi mulki ana canza dala daya akan naira 184 zuwa 185 amma yanzu ana sayen dala daya a kan Naira 750, a cewar Garkuwa.

A lokacin da ta ke bayani kan yadda canjin kudi ya shafi farashin kayayyaki a kasuwa, Madam Elizabeth Sudan, ta bayyana cewa, kudin kaya a kasuwanni ya karu, domin a kwanakin baya ta sayi fakitin sinadarin Maggi na dandanon miya kan naira 750 amma ya koma naira 800, buhun shinkafa ya tashi daga dubu 40 zuwa dubu 44, kuma ko ina aka je sai a ce dalar Amurka ta yi tsada.

A nashi bayanin, masanin tattalin arziki Yusha'u Aliyu, yana ganin akwai matsalar da ya kamata a magance idan bankin CBN ya kashe wadannan kudaden kuma darajar naira ba ta hau ba.
VOA 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki