An Bukaci Shugaban NAHCON Ya Bada fifikon Kawo Sauyi da Tabbatar Da Tsantsaini
Sabon shugaban hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullah Saleh, ya samu sakon taya murna daga hukumar gudanarwar ta (Nigeria Hajj and Umrah Special Info) inda suka bayyana kwarin gwuiwarsu cewar Pakistan na iya jagorantar hukumar ta hanyar gaskiya da rikon amana. A cikin sakon, kungiyar ta taya Farfesa Saleh Pakistan murna kan nadin da aka yi masa, inda ta bayyana shi a matsayin wani gagarumin nauyi da ke zuwa a wani lokaci mai muhimmanci ga hukumar. Sanarwar ta bayyana kalubalen da magabacinsa ya fuskanta da suka hada da zargin cin hanci da rashawa, sannan ta jaddada muhimmancin maido da amana a cikin hukumar ta NAHCON. Shugabannin gudanarwar kuniyar sun shawarci Farfesa Abdallahi Pakistan da ya ba da fifiko wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a dukkan ayyuka, inda suka bayar da shawarar samar da ingantacciyar hanyar sa ido domin kare kai daga cin hanci da rashawa da kuma kara sahihancin hukumar. Don tabbatar da jagoranci mai in...